For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Buhari Zai Kai Ziyarar Aiki Kaduna

Ana sa ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da aiyuka a yayin ziyarar wuni biyun da zai kai jihar Kaduna, wadda za ta fara Alhamis din nan ta kuma kare a gobe Juma’a.

Jaridar The Guardian ta rawaito cewa, Shugaban Kasar wanda zai ziyarci manyan garuruwan Kaduna, Zaria da Kafanchan, mukarraban gwamnati za su zagaya da shi wajen aiyukan tituna wadanda gwamnatin Nasir El-Rufa’i ta yi.

KU KARANTA: Kungiyar Kwadago Ta Sanya Sharadi Kafin A Cire Tallafin Mai

Mai Bayar da Shawara na Musamman ga Gwamna El-Rufa’i kan Kafofin Yada Labarai, Muyiwa Adekeye, ya bayyana cewa, Shugaban Kasar zai kuma kaddamar da gadar sama ta Kawo, wadda aka sabunta da kuma titin WAFF da aka mai da shi mai hannu biyu.

Comments
Loading...