Mashawarci na Musamman ga Shugaban Kasa a kan Harkokin Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Femi Adesina ya ce, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai sanyawa Kudirin Dokar Zabe hannu.
Femi Adesina ya baiyana hakan ne a yau Talata ta cikin shirin talabijin na Sunrise Daily, wanda gidan talabijin na Channels suka gabatar.
Ya ce, “Zai iya yiwuwa yau, zai iya yiwuwa gobe, zai iya yiwuwa kowanne lokaci, amma cikin wa’adin kwanaki 30.”
“Za a iya sanya masa hannu yau; za a iya sanya masa hannu gobe. Cikin awanni, ba kwanaki ba. Awannin za su iya zama 24, za su iya zama 48; amma ba kwanaki ko makonni ba.
Da yake kare mai gidansa, Femi ya kushe masu kalubalantar Buhari kan jinkirin sanyawa kudirin hannu, inda ya ce har yanzu shugaban bai fi ce daga wa’adin da kundin tsarin mulki ya ba shi ba.
“Ka san kafin Shugaban Kasa ya sanya abin rubutu a takarda kan kowacce doka, musamman ma wannan da ke da alaka da harkokin zabenmu, akwai bukatar a duba a sake dubawa.
“Sai ya nemi ra’ayoyin masu ruwa da tsaki, idan ya gamsu da cewa a tsefe komai ba zai aikata kuskure ba, sannan sai ya sanya hannu. Kuma ina fadawa ‘yan Najeriya cewar, za su ji bayani game da wannan kudirin dokar zabe cikin awanni masu zuwa,” in ji shi.
Shugaba Buhari dai yana da wa’adin ranar Talata 1 ga watan Maris ne, da idan bai sanya hannun ba Majalissar Tarayya za ta iya gaban kanta a game da dokar.