A ranar Litinin din nan, Shugaba Buhari zai tashi zuwa birnin Riyadh na kasar Saudiyya domin halartar taro kan sanya hannun jari wanda wata cibiyar horaswa kan sanya hannun jari da ake kira da ake kira Future Investment Initiative Institute ta shirya.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Babban Mai Temakawa Shugaba Buhari kan Harkokin Yada Labarai, Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren Lahadi.
Garba Shehu ya ce, Shugaban zai samu halartar taron ne a karo na biyar da fara taron wanda shugabannin kasuwanci daga Nigeria, ma’aikatan banki, shugabannin kamfanoni, masana harkokin makamashi ke halarta domin tattaunawa kan yanda za a habbaka sanya hannun jari a duniya.
Ya kara da cewa, taron da za a debe kwanaki 3 ana gabatarwa mai taken ‘Sanya Hannun Jari a Al’umma (Investment in Humanity)’ zai samu halartar manyan shugabannin harkokin kasuwanci na duniya, wanda kuma za a tattauna kan cigaban da ake samu a harkar makamashi, kakkarfan sanya hannun jari na gaskiya, amfani da kimiyya, da kuma tasirin sauyin yanayi kan al’umma da sauran batutuwa.
“Shugaba Buhari zai yi aikin Umarah a Madina da Makka kafin ya dawo kasa a ranar Juma’a”, in ji Sanarwa.
Sanarwar ta kuma ce, Shugaba Buhari zai sami rakiyar Ministan Harkokin Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Dr. Isa Ibrahim Pantami, Karamin Ministan Harkokin Kasashen Waje, Amb. Zubairu Dada, Karamin Ministan Harkokin Man Fetur, Chief Timipre Sylva, Mai Bayar da Shawara na Kasa kan Harkokin Tsaro, Maj. Gen Babagana Monguno, Babban Daraktan Hukumar Bincike kan Harkokin Tsaro, Amb. Ahmed Rufai Abubakar, Daraktan Kula da Hukumar Sanya Hannun Jari na Cikin Nigeria, Uche Orji, da kuma Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Nigeria Mazauna Kasashen Waje, Hon. Abike Dabiri-Erewa.
Sanarwar ta kuma ce wadansu da za su kasance cikin masu bayar da gudunmawa a taron daga kamfanoni masu zaman kansu a Nigeria sun hada da, Alhaji Mohammed Indimi, Alhaji Aliko Dangote, Tope Shonubi, Wale Tinubu, Alhaji Abdulsamad Rabiu, Hassan Usman, Omoboyode Olusanya, Abubakar Suleiman, Herbert Wigwe da kuma Leo Stan Ekeh.