For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Buhari Zai Yi Wa Ƴan Ƙasa Jawabi Kan Ranar Demokaraɗiyya A Gobe Lahadi

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga ƴan ƙasa a gobe Lahadi, 12 ga watan Yuni, 2022, da misalin ƙarfe 7 na safe domin taya murnar zagayowar ranar demokaraɗiyyar Najeriya.

Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai, Femi Adesina ne ya sanar da hakan a wata gajeruwar sanarwa da ya fitar a yau Asabar.

Ya yi kira ga dukkan kafafen yaɗa labarai da su haɗa da gidan talabijin na ƙasa, NTA, da Gidan Radiyo Najeriya domin watsa jawabin Shugaban ga ƴan ƙasa baki ɗaya.

Comments
Loading...