Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yiwa ‘yan Najeriya jawabin ban kwana daga karagar mulkin Najeriya a gobe Lahadi da misalin karfe 7 na safe.
Sanarwar da Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara na Musamman kan Harkokin Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Femi Adesina ya fitar, ta yi kira ga gidajen radio da talavision da sauran kafafen yada labarai da su hada da NTA domin watsawa ‘yan kasa jawabin.