For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

BUK, FCE Kano Da COE Minna Zasu Fara Sabin Kwasakwasai

Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa, NUC ta amince da fara karatun sabon kwas a Jami’ar Bayero da ke Kano, BUK, inda jami’ar za ta fara gabatar da BA Shariah.

Haka kuma baya da BUK, Hukumar ta amince da kwasakwasai 11 da kwalejojin ilimi guda biyu za su gudanar karkashin kulawar wasu jami’o’in.

Kwalejojin ilimin da aka amincewa su gudanar da kwasakwasan sune, Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya da ke Kano wato FCE, Kano, da kuma Kwalejin Ilimi ta Minna da ke jihar Niger.

Kwasakwasan da aka amincewa FCE, Kano sune B.A. (Ed.) Islamic Studies, B.Sc. (Ed.) Biology Education, da kuma B.Sc(Ed) Chemistry Education.

Hukumar ta kuma amincewa COE, Minna, fara gudanar da wadannan kwasakwasai: B.A. (Ed.) History Education, B.A. (Ed.) Hausa Education, B.A. (Ed.) Arabic Education, B.A. (Ed.) Islamic Studies, B.Sc. (Ed.) Biology Education, B.Sc. (Ed.) Mathematics Education, B.Ed. Social Studies da kuma B.A. (Ed.) English Education.

Comments
Loading...