For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

BUK Ta Samarwa Ɗalibanta Aikin Da Zasu Na Samun Naira 15,000 Duk Wata

Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano, BUK, Farfesa Sagir Adamu Abbas ya bayyana cewa, jami’ar ta ɓullo da tsarin samar da aikin yi ga ɗalibai.

Farfesa Sagir ya ce, jami’ar ta ɗauki ɗalibai wani aiki da zasu na yi mata ana biyansu naira 15,000 duk wata.

Ya bayyana hakan ne a ƙarshen makon da ya gabata, lokacin da ya karɓi baƙuncin wakilan Ƙungiyar Ƴanjaridun Ɓangaren Ilimi ta Najeriya, ECAN, a ofishinsa da ke jami’ar.

Farfesan ya bayyana cewar, wannan tsarin da jami’ar ta ɓullo da shi, ba ya kawo matsala ga karatun ɗaliban saboda ƙarancin lokacin da yake buƙata, inda ya ce aikin ba ya wuce, share-share ko wasu ƙananan aiyuka da ba su da wahala.

Da yake magana a kan ƙarin kuɗin makaranta da jami’ar ta yi, Farfesa Sagir ya koka kan tsadar kuɗaɗen gudanar da jami’ar musamman ma wajen samar da makamashin lantarki a jami’ar.

Ya bayyana cewar, kuɗin shan wutar lantarki a jami’ar duk wata yana kaiwa naira miliyan 35, yayin da kuɗin siyan man dizel domin sa wa a injinan bayar da wuta ya kan kai naira miliyan 40 a wata guda.

Shugaban Jami’ar ya ce, dole ce ta sa jami’ar yin ƙarin kuɗin rijistar domin ta samu damar samar da abubuwan da ake buƙata ga ɗaliban da yawansu ya kai 45,000 da kuma malamai da ma’aikatan da yawansu ya haura 5,000.

Comments
Loading...