Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Education
DA ƊUMI-ƊUMI: Tinubu Ya Ce Manyan Makarantu Su Dakatar Da Ƙarin Kuɗin Makarantar Da Suka Yi
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci shugabannin makarantun gaba da sikandire na Gwamnatin Tarayya da su guji ƙarin kuɗaɗen makaranta da ake biya da kuma duba yiwuwar gujewa ƙarin a nan gaba don kar iyaye su fuskanci ƙarin shiga cikin!-->…
Tsohon Rijistaran NECO Ya Zama Shugaban Jami’ar Khalifa Isyaka Rabiu University
Tsohon Shugaban Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa, NECO, Farfesa Abdulrashid Garba ya zama Shugaban Jami’ar Khalifa Isyaka Rabiu University, KHAIRUN, na farko.
KHAIRUN dai na ɗaya daga cikin sabbin jami’o’i masu zaman kansu a Kano da suka!-->!-->!-->…
Ƙungiyar WAMY Zata Gina Jami’ar Musulunci A Jigawa
Ƙungiyar Taron Matasa Musulmi ta Duniya, WAMY, ta yi alƙawarin gina gagarumar jami’ar Musulunci a Jihar Jigawa.
Wannan ƙudiri na WAMY ya bayyana ne lokacin Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi ya ziyarci ofishin ƙungiyar da ke Kano a jiya!-->!-->!-->…
Wani Gwamna Ya Amince Da A Ɗebi Sabbin Malaman Makaranta A Jiharsa
Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya amince da a ɗebi malaman firamare, ƙananan ma’aikatan ofis da masu gadi a ƙananan hukumomi 22 na jihar.
Shugaban Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi ta Najeriya, ALGON reshen Jihar Delta, Victor Ebonka!-->!-->!-->…
Ɗan Majalissar Jigawa Mai Wakiltar Birnin Kudu Zai Nemawa Matasa Guraben Karatu
Ɗan Majalissar Jihar Jigawa mai wakilatar Mazaɓar Birnin Kudu, Muhammad Kabir Ibrahim ya yi alƙawarin nemawa matasan mazaɓarsa guraben karatu a Kwalejin Horar da Malamai ta Jihar Jigawa da ke Gumel.
Ɗan Majalissar ya bayyana hakan ne a!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya Ta Ce A Dinga Amfani Da Harsunan Uwa A Koyarwa
A jiya Alhamis ne wani babban jami’in Ma’aikatar Ilimi ya ce, Gwamnatin Tarayya za ta inganta amfani da harsunan uwa wajen koyarwa, musamman a a makarantun firamare da ƙaramar sikandire.
Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi, David Adejo ne!-->!-->!-->…
Ƙara Kuɗin Makaranta; Anya Kuwa Ba A Tsokano Wata Fitinar Ba?
Daga: Hafsat Abubakar Sadiq
A baya bayan nan, ƙarin kuɗin makaranta da aka samu musamman ga ɗaliban wasu Jami’oin Tarayya ya bar baya da ƙura.
Wannan mataki da aka ɗauka, ba kaɗai ɗalibai ya shafa ba, har ma da uwa-uba iyaye. A!-->!-->!-->!-->!-->…
An Kori Malaman Jami’a Biyu Saboda Zargin Aikata Baɗala
Shugaban Jami’ar Abuja, Farfesa Abdulrasheed Na’Allah ya ce, jami’ar ta kori malamanta guda biyu saboda zarginsu da aikata baɗala a kwanan nan.
Shugaban ya kuma faɗawa wakilin jaridar PUNCH cewa, jami’ar ta tsara wata kafa ta musamman!-->!-->!-->…
Wasiƙa Ga Gwamnan Jigawa, Umar Namadi Kan Gyaran Ilimi
Daga: Haruna Shu’aibu Ɗanzomo
Maigirma Gwamna, da fatan kana cikin ƙoshin lafiya, Allah ya sa haka, amin.
Tabbas hankali yana kan abubuwa guda uku a Jihar Jigawa wanda tsawon mulkinku na shekaru 8 wato daga 2015 zuwa 2023 sam ba ku!-->!-->!-->!-->!-->…
Gwamnatin Kano Zata Bayar Da Tallafin Karatu Ga Masu 1ST Class A Jihar
Gwamnatin Jihar Kano ta dawo karbar takardun ‘yan asalin jihar wadanda suka cancanci samun tallafin zuwa karin karatu.
Gwamnatin jihar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar, Malam Sunusi!-->!-->!-->…
Bawa Dalibai Bashin Karatu, Zai Iya Durkusar Da Ilimi A Arewacin Najeriya
Daga: Ahmed Ilallah
Kafin mu soma batu a kan wannan al’amari ya kamata duk mai bibiyar kudurorin gwamnati a kan harkar ilimi musamman na manyan makarantu, ya san a kwai shirin da gwamnatin baya ta yi a kudundune, duk da kokarin wayar da!-->!-->!-->…
DA DUMI-DUMI: Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Dokar Baiwa Dalibai Bashi
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sanya hannu a kan kudirin dokar baiwa dalibai bashi wanda hakan ya tabbatar da tsarin a matsayin doka.
Mai temakawa shugaban kasa, Dele Alake ne ya bayyana haka ga ‘yan jaridun Fadar Shugaban Kasa a yau!-->!-->!-->…
Damar Yin Karatu Kyauta A University of Dundee Da Ke Ingila
Gidauniyar Steve Weston and Trust Scholarship ta dalibai ‘yan Nahiyar Afirka, ‘yan Amurka da ‘yan Asiya ce, wadanda suke son dora a karatunsu a matakin gaba da digiri na farko a University of Dundee.
Damar zata baiwa dalibi ko daliba!-->!-->!-->…
Shugaban Jami’a Ya Baiwa Dalibi Damar Yin Karatun Likitanci Kyauta Bayan Ya Fi Kowa Cin JAMB A…
Shugaban Jami’ar Godfrey Okoye University (GOU), Enugu, Rev. Fr. Christian Anieke, ya bayar da cikakkiyar damar karantar likitanci kyauta a jami’arsa ga Lotanna Azuokeke wanda ya fi kowa cin jarabawar JAMB ta bana.
Lotanna Azuokeke, dan!-->!-->!-->…
Masu Rubuta JAMB Sun Je Jarabawa Da Wukake, Sun Yi Barazanar Maganin Shugabannin Jarabawar
Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB, ta ce masu rubuta JAMB sun yi amfani da wukake wajen yin barazana ga jami’an hukumar.
Zargin ya biyo bayan rahotannin da suka nuna cewa, JAMB ta tabbatar da cewa, masu rubuta!-->!-->!-->…
Gwamnati Ta Dakatar Shugaban Hukumar Kula Ilimin Sakandire Saboda Zargin Cinhanci
An dakatar Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Sakandire ta Kasa, NSSEC, Farfesa Benjamin Abakpa saboda zargin badakalar kudade.
Dakatarwa ta bayyana ne a takardar da Babban Sakatare na Ma’aikatar Ilimi ta Kasa, Andrew David Adejo ya!-->!-->!-->…
JAMB Ta Kara Wa’adin Cike DE
Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB, a jiya Litinin ta kara wa’adin cike form na DE na bana da karin sati daya.
A jawabin da hukumar ta saki, Mai Magana da Yawun JAMB, Dr. Fabian Benjamin ya ce, an fara rijistar DE!-->!-->!-->…
Dalibai Na Son JAMB Ta Fadada Bayar Da Damar Yin Rijista
Shugabancin Kungiyar Dalibai ta Najeriya, NANS, a yau Alhamis ta yi kira ga Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB da ta fadada bayar da damar yin rijistar DE a dukkan fadin kasa.
Kiran na JAMB wanda ya fito daga!-->!-->!-->…
Ko Akwai Bukatar A Riƙa Tantance Malamai Kafin Su Fara Wa’azi A Najeriya?
Sananniyar kafar yada labarai ta BBC ta yi bincike tare da jin ra’ayoyin malamai daban-daban kan ko akwai bukatar a dinga tantance malamai kafin a ba su dama su yi wa’azi ga al’umma.
Wannan ya samo asali ne saboda zargin sakin kalaman!-->!-->!-->…
Za A Yi Muhawara Da Sheikh Idris Dutsen Tanshi Da Malamai Kan Zargin Munana Kalamai Ga Manzon Allah…
Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi ta yi ƙarin haske a kan dalilanta na ɗage zaman tattaunawa da ta shirya da Sheikh Idris Abdul’aziz, wanda ake zargi da munana kalamai a kan Annabi Muhammadu.
Tun farko a yau Asabar ne, hukumar!-->!-->!-->…