Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Lead Story
Yanzu Mu Muke Da Cikakken Iko Da Jihar Rivers – PDP
Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP ta bayyana cewar ita ke da cikakken iko da Jihar Rivers, inda tai alfaharin cewa, Gwamnan jihar Siminalayi Fubara da jam’iyyar ke riƙe da madafun ikon siyasar jihar.
A wata sanarwa da Sakataren!-->!-->!-->…
Ba Zai Yiwu Ka Ƙaƙabawa Mutane Haraji Ba Tare Da Ƙara Musu Kuɗin Da Suke Samu Ba – Ndume
Sanata Ali Ndume ya kushe batun sabon haraji na kula da hadahadar banki ta intanet, inda ya ce, rashin dacewa ne gwamnati ta cigaba da cajar ‘yan ƙasa haraje-haraje ba tare da ta yi wani abu da zai ƙara musu kuɗin shigar da suke samu ba.
!-->!-->…
Tsarin Shugaban Ƙasa Ba Shi Da Amfani A Najeriya, A Koma Tsarin Firaminista, In Ji Wani Ɗan…
Wani ɗan Majalissar Wakilai mai suna Abdussamad Dasuki ya ce, tsarin da ake kai na shugaba mai cikakken iko a Najeriya ba ya temakon Najeriya, ya kamata a yi watsi da shi a dawo tsarin firaminista irin wanda aka yi a jamhuriya ta farko.
!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya Zata Sauƙaƙa Hanyar Samun Asusun Bankuna Ga Waɗanda Ba Su Da Su
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana tsare-tsaren gwamnantin tarayya domin rage talauci da matsalar tsaro a faɗin ƙasa ta hanyar shigar da ƴan Najeriya cikin harkokin samun kuɗaɗe.
Fadar ta bayyana cewar akwai muhimman tattaunawa da ake yi!-->!-->!-->…
Rikicin Cikin Gidan Da Ke APC Da PDP Ya Fi Na Labour Party – Peter Obi
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi a jiya Laraba ya bayyana cewar jam’iyyarsu zata magance matsalolinta na cikin gida tare da samun ƙarin ƙarfi.
Peter Obi wanda yake jawabi ga manema labarai Ya!-->!-->!-->…
Yahaya Bello Ya Yi Amfani Da Sama Da Dala 720,000 Na Jiha Wajen Biyan Kudin Makarantar Ɗansa
Shuagaban Hukumar EFCC, Oala Olukayode ya bayyana cewar, tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya fitar da kuɗi kimanin dala dubu 720,000 daga asusun gwamnatin jihar domin biya wa ɗansa kuɗin makaranta na shekaru masu zuwa.
A lokacin!-->!-->!-->…
Ganduje Na Tsaka Mai Wuya, Sabbin Shugabannin Mazaɓarsa Sun Ƙara Dakatar Da Shi Daga APC
Rikicin da ya dabaibaye jam’iyya mai mulki, All Progressive Congress, APC a Jihar Kano ya ƙara ɗaukar sabon salo, inda sabbin waɗanda suka bayyana a matsayin shugabannin Mazaɓar Ganduje suka fitar da sabuwar sanarwar dakatara da Shugaban!-->…
Litar Man Fetur Zata Dawo Naira 500 Idan Matatar Mai Ta Port Harcourt Ta Fara Aiki A Kwanannan
A daidai lokacin da ma’aikatan matatar mai ta Port Harcourt ke rige-rige wajen ganin sun kammala aikin daidaita matatar domin fara fitar da tataccen mai, dillalan man fetur na shiryawa domin fara saro man fetur daga matatar.
A ranar!-->!-->!-->…
An Yi Kira Ga JAMB Da Ta Sauƙaƙa Hanyar Yin Regularization Ga Masu Cike DE
Hukumar Shiraya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB ta ce duk dalibin da ya zaɓi ya sami addmission ba ta ingantacciyar hanya ba zai fuskanci.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da JAMB ke jaddada cewar, duk wani admission na shiga!-->!-->!-->…
Gwamnatin Kano Ta Maka Ganduje, Ɗansa Da Matarsa A Kotu Kan Zargin Badaƙala Da Kuɗaɗe
Gwamnatin Jihar Kano ta maka tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Hafsat Umar da ɗansa Umar Abdullahi Umar da wasu mutane biyar a kotu kan zarge-zarge guda takwas da suke da alaƙa da cinhanci da rashawa, badaƙala da!-->…
NATO Na Bikin Cika Shekaru 75 Da Kafuwa
Ministocin ƙasashen waje na rundunar NATO wadda aka kafa a shekarar 1949 domin magance barazanar sojojin rusashshiyar Tarayyar Sobiyat ga kasashen Turai sun taru domin murnar cikar rundunar shekaru 75 da kafuwa.
Bikin dai ya gudana ne!-->!-->!-->…
Shugaban Miyatti Allah Ya Ce Ba Shi Da Wata Alaƙa Da Ta’addanci
Shugaban Miyatti Allah Kautal Hore, Alhaji Bello Bodejo, wanda ke fuskantar tuhume-tuhumen ta’addanci ya buƙaci kotu da ta bayar da belinsa, inda ya ce ba shi da wani tarihi na aikata ta’addanci.
Bodejo wanda ke fuskantar tuhuma a!-->!-->!-->…
Malam Adamu Foundation Zata Ɗau Nauyin Karatun Ɗaliban Jigawa A Khadija University Majia
Gidauniyar Malam Adamu Foundation (MAF) ta Alhaji Musa Adamu Majia mamallakin Jami’ar Khadija da ke Majia a Jihar Jigawa zata ɗau nauyin karatun ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi a Khadija University Majia.
MAF ta tanadi ɗaukar nauyin karatun!-->!-->!-->…
Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Ɗaurin Shekaru 5 Kan Farouk Lawan
Kotun Ƙoli ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekaru biyar kan tsohon Ɗan Majalissar Wakilai, Farouk Lawan bisa kama shi da laifin karɓar cin hanci na dala 500,000 daga sanannen ɗan kasuwar nan Femi Otedola.
An dai binciki Farouk Lawan ne!-->!-->!-->…
Soja Na Samun Ƙasa Da Naira 50,000 A Wata – In Ji Babban Hafsan Sojojin Najeriya
Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Janaral Christopher Musa ya bayyana cewar ana biyan sojojin Najeriya albashin naira 50,000 ne a kowanne wata, yayin da shi kansa da sauran sojoji ke samun naira 1,200 a matsayin alawuns na aiki a kowacce!-->…
PDP Ta Buƙaci INEC Ta Sanya Lokacin Gudanar Da Zaɓen Cike Guraben Ƴan Majalissu 25 Na Jihar Rivers
Jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta yi kira Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, da ta sanya ranar gudanar da sabon zaɓen cike guraben ƴan majalissun Jihar Rivers 25 da suka fice daga jam’iyyar suka koma jam’iyyar APC.
!-->!-->!-->…
JAMB Ta Ƙara Kuɗin Rijistar Jarabawa
Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB ta ƙara kuɗin rijistar yin jarabawar UTME zuwa naira 7,700 da kuma naira 6,200.
Sanarwar ƙarin kuɗin ta fito ne daga hukumar shirya jarabawar a shafinta na X, inda ta sanar da fara!-->!-->!-->…
Kotun Ƙoli Ta Sanya Ranar Sauraron Ɗaukaka Ƙara Kan Zaɓen Kano
Kotun Ƙolin Najeriya ta sanya ranar Alhamis 21 ga watan Disambar nan domin fara sauraron ɗaukaka ƙarar da aka yi kan zaɓen gwamnan Jihar Kano wadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shigar.
Wannan rana na ɗauke ne a sanarwar da kotun ta aike!-->!-->!-->…
Yanda Aka Raba Kuɗaɗen Da Aka Samu A Watan Nuwamba Tsakanin Gwamnatin Tarayya, Jihohi Da Ƙananan…
Kwamitin Rarraba Kudaden Tarayya, FAAC, ya raba kuɗaɗen da aka samu a watan Nuwamba kimanin naira tiriliyan 1.088.783 ga Gwamnatin Tarayya, gwamnatocin jihohi da kuma ƙananan hukumomi.
Wannan ya bayyana ne a rahoton da kwamitin FAAC ya!-->!-->!-->…
Gwamnatin Jigawa Ta Dakatar Da Biyan Ƴan J-Teach, Ta Kuma Gano Malaman Bogi 240 Da Masu Takardun…
Gwamnatin Jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umar Namadi ta sanar da dakatar da biyan dukkan malaman da suke koyarwa a makarantun jihar ƙarƙashin shirin J-Teach.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Sagir Musa ne!-->!-->!-->…