Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Lead Story
Ana Matsawa Najeriya Kan Ta Amince Da Auren Jinsi
Cocin Angalican ta Najeriya ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bijirewa kiraye-kirayen da Turawan Yamma ke mata na ta sake matsayinta kan auren jinsi a Najeriya.
Wannan dai na a cikin jawabin bayan taron da cocin ta saki bayan!-->!-->!-->…
Kwanannan Naira Zata Farfaɗo, Masu Dala Zasu Tafka Asara – CBN
Akwai ƙwararan alamu da ke nuni da cewar, Babban Bankin Najeriya, CBN, ya shirya domin ɗaukar matakan farfaɗo da darajar naira a ƴan kwanaki masu zuwa kaɗan.
Wannan ci gaba dai idan ya tabbata, ana sa ran zai jawo faɗuwar farashin dala!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: NLC Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Matuƙar Aka Ƙara Kuɗin Mai
Ƙungiyar Ƙwadago, NLC, ta yi barazanar tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani a duk faɗin Najeriya matuƙar aka ƙara kuɗin man fetur daga naira 617 da ake siyarwa a yanzu.
Ƙungiyar ta bayyana yunƙurin ƙarin da take ji ana yi a matsayin!-->!-->!-->…
Mazaɓun Sanatoci 6 Da Ba Su Taɓa Yin Gwamna Ba Tun 1999
Binciken da DAILY TRUST ta yi ya nuna cewar akwai aƙalla mazaɓun sanatoci guda 6 a Arewacin Najeriya da ba su taɓa fitar da gwamna a jihohinsu ba tun dawowar mulkin demokaraɗiyya a shekarar 1999.
Mazaɓun sune, Mazaɓar Benue ta Kudu,!-->!-->!-->…
Kwanannan Za A Koma Siyar Da Litar Fetur Naira 720 Saboda Faɗuwar Darajar Naira
Masu siyar da mai sun nuna cewar farshin man fetur zai tashi daga yanda yake a yanzu ya koma tsakanin naira 680 zuwa 720 a kwanaki masu zuwa matuƙar aka ci gaba da canja dala a kan naira 910 zuwa 950 a guraren canjin kuɗaɗe.
Su kuma!-->!-->!-->…
Gwamnatina Zata Magance Matsalar Tsaro A Najeriya – Shugaba Tinubu
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce, gwamnatinsa zata tanadi abubuwan da ake buƙata domin ƙara ƙarfin jami’an tsaro da samar musu da ƙarin walwala a sabon ƙudirinta na magance matsalar tsaro da sauran abubuwan da ke da alaƙa da shi a!-->…
El-Rufai Ya Haƙura Da Muƙamin Minista, Ya Tura Sunan Madadinsa
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya janye daga buƙatar zama ɗaya daga cikin ministocin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kamar yanda jaridar PREMIUM TIMES ta gano.
Wata majiya daga Fadar Shugaban Ƙasa ta ce, El-Rufai ya!-->!-->!-->…
Wasu Sanatocin Sun Samu Naira Miliyan Biyu Ta Shiga Hutunsu – Sanata Ningi
Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Mazaɓar Sanata ta Bauchi ta Tsakiya ya ce, wasu ƴan majalissar sun samu naira miliyan biyu a matsayin kuɗin alawus na hutunsu, duk da dai shi bai samu nasa ba.
A wani yanayi da sanatocin ba su so ba,!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Zamu Kashe Bazoum Matuƙar Aka Kawo Mana Hari – Sojojin Nijar
Rayuwar hanɓararren Shugaban Ƙasar Nijar, Mohammed Bazoum na cikin hatsari saboda barazanar da waɗanda suka hamɓarar da shi kuma suke riƙe da shi suka yi, ta cewar zasu kashe shi matuƙar ECOWAS tai ƙoƙarin tura sojoji don su dawo da!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: ECOWAS Ta Bayar Da Umarni Sojoji Su Yaƙi Masu Juyin Mulkin Nijar
Ƙungiyar Ci Gaban Tattalin Arziƙin Africa ta Yamma, ECOWAS, ta bayar da umarni ga sojojinta da ke jiran umarni da su farmaki masu juyin mulki a Nijar domin dawo da amfani da kundin tsarin mulkin ƙasar.
Jagoran ECOWAS, Omar Alieu Touray!-->!-->!-->…
‘Dole Ne Mu Yi Amfani Da Tattaunawa’ – Bola Tinubu A Buɗe Taron ECOWAS Na 2 Kan Juyin Mulki A Nijar
Shugaban Najeriya, kuma Shugaban Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arziƙin Africa ta Yamma, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabin buɗe taron ECOWAS karo na biyu kan juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar.
A cikin jawabin nasa,!-->!-->!-->…
Ƴan Najeriya Sun Kashe Naira Tiriliyan 3.33 A Kira Da Data A 2022
Ƴan Najeriya da sauran masu amfani da netwok a Najeriya sun kashe naira tiriliyan 3.33 a kira, saka data, tura saƙon kar ta kwana da sauran abubuwan da ake da netwok a cikin shekarar 2022, in ji Hukumar Sadarwa ta Najeriya, NCC.
Wannan!-->!-->!-->…
Jihar Kano Na Buƙatar A Cire Jihohi 2 Daga Cikinta – Sanata Doguwa
Mataimakin Shugaban Majalissar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya tabbatarwa da masu neman Jihar Tiga da Jihar Gari daga cikin Jihar Kano cewar, Majalissar Tarayya za tai musu adalci a lokacin gyaran kundin tsarin mulki.
Sanata Barau!-->!-->!-->!-->!-->…
JUYIN MULKI: Sarki Sunusi Lamido Ya Haɗu Da Sojoji Masu Mulkin Nijar
Sarkin Kano Mai Murabus, Alhaji Muhammadu Sunusi ya haɗu da shugabannin mulkin soja na Nijar a ƙasar ta Nijar ana tsaka da matsin lamba kan a dawo da Shugaba Mohammed Bazoum.
Sarkin wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN ne,!-->!-->!-->…
Yawan Dogaro Da Bashi Ya Zo Ƙarshe A Najeriya – Tinubu
A jiya Talata ne a Abuja, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Tsare-tsaren Kashe Kuɗaɗe da Sake Fasalin Karɓar Haraji, inda ya ce, yawan dogaro da bashi wajen kashe kuɗaɗen gudanar da gwamnati ya zo!-->…
Amurka Ta Ce In Aka Takura Mata Zata Mamayi Nijar
Ƙasar Amurka ta yi gargaɗi ga sojojin da ke mulki a Nijar da cewar, matuƙar ba a dawo da bin kundin tsarin mulkin ƙasar ba, to zata mamaye ƙasar.
Mai Riƙon Muƙamin Mataimakiyar Sakatariyar Harkokin Waje ta Amurka, Victoria Nuland ce ta!-->!-->!-->…
PDP Ta Ƙirƙiri Kwamiti Na Musamman Kan Zaɓen Jihohin Bayelsa, Imo Da Kogi
A daidai lokacin da zaɓen gwamnoni na ranar 11 ga watan Nuwamba wanda za a yi a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi ke ƙara ƙuratowa, Jam’iyyar PDP ta ƙirƙiri kwamiti na musamman kan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a kan manufofin jam’iyyar da!-->…
Gwamnati Ta Janye Ƙarar Da Ta Kai Shugabannin Ƙwadago, Akwai Yiwuwar Fasa Yajin Aikin Da Za A Fara…
A jiya Litinin Gwamnatin Tarayya ta janye ƙarar da ta kai Ƙungiyar Ƙwadago, NLC, da Ƙungiyar Ƴan Kasuwa, TUC, tana zarginsu da saɓa umarnin kotu, inda suka gudanar da zanga-zanga a ranar 2 ga watan Agusta, 2023, kan janye tallafin man!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Sanatoci Sun Cire Sunan El-Rufa’i Da Wasu Mutum Biyu Daga Ministocin Tinubu
Sunan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi ɓatan dabo a cikin jerin sunayen ministocin da sanatoci suka tabbatar a yau Litinin.
Haka kuma a cikin sunayen ba a ga sunan Sanata Abubakar Danladi daga Jihar Taraba ba da kuma na!-->!-->!-->…
Ganduje Ya Shirya Karɓar Kwankwaso A APC, Ya Ce Kyakkyawan Ɗan Siyasa Ne
Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana shirinsa na karɓar Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso matuƙar ya yarda ya shiga jam’iyyar.
Ganduje ya yi wannan magana ne a lokacin da yake!-->!-->!-->…