Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
News
CAC Ta Gargaɗi Masu POS Da Ba Su Yi Rijista Ba, Ta Ce Ana Iya Rufe Asusunsu
Hukumar CAC ta gargadi masu gudanar da kasuwancin POS da ba su yi rijista ba yayin da wa’adin da aka ba su ya ƙare.
Tun a baya dai aka sanar da su wa’adin yin rijista da aka ayyana tun ranar 7 ga Yuli, 2024, kuma wa’adin ya cika a ranar!-->!-->!-->…
Iya Masu NIN Number Ne Zasu Mori Sayen Shinkafa Kan Farashin Naira 40,000
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kawai mutanen da ke da Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa ta NIN ne za su samu damar sayen buhun shinkafa mai nauyin 50kg a farashin N40, 000 a matsayin wani bangare na tallafin abinci ga ƴan Najeriya.
Shugaban!-->!-->!-->…
Sai Ranar 15 Ga Satumba Man Ɗangote Zai Shiga Gidajen Man Najeriya – NNPC
Matatar Man Fetur ta Dangote zata fara cika kasuwar man fetur da mai daga ranar 15 ga Satumba, 2024, kamar yanda Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPCL, ya sanar.
Sanarwar da Olufemi Soneye, Jami’in Hulda da Jama’a na NNPCL ya!-->!-->!-->…
Ƴanbindiga Sun Kama Mutum 22 A Wani Sabon Hari A Kaduna
A wasu hare-hare daban-daban da aka kai, ƴan bindiga sun sace mutum 19 a unguwar Mani kusa da wani kamfani a Mazaɓar Rido da ke Ƙaramar Hukumar Chikun da kuma yankin Danhonu II Millennium City a Kaduna.
A garin na Mani, ƴan bindigar sun!-->!-->!-->…
Wasu Fitattun Mutane Sun Zama Shugabannin Ƙungiyar One Voice Development Initiative
Ƙungiyar One Voice Development Initiative ke da muradin inganta shugabanci na gari, nuna gaskiya a harkokin jama'a, da ci gaban siyasa, ta sanar da sabbin shugabanninta na ƙasa.
Abbas Abdullahi, CISSP, IPMA, ne ya zama shugaban ƙungiyar!-->!-->!-->…
Ƴan Najeriya 9 Da Aka Tabbatar Da Sunayensu Don Karɓar Kyautar Ballon d’Or
Kyautar Ballon d'Or ce mafi girman nasarar kowane ɗan wasan ƙwallon ƙafa, wadda ake bayarwa duk shekara ga mafi kyawun 'yan wasa mata da maza a duniya.
Tun daga kafuwarta a shekarar 1956, ta zama alamar babbar lambar yabo da kowane ɗan!-->!-->!-->…
YANZUNNAN: Mutum 2 Sun Mutu, 2 Sun Jikkata A Rugujewar Gini A Kano
Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane biyu da jikkatar wasu biyu a lokacin da wani bene mai hawa biyu ya rufta a unguwar Noman’s Land, da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a Jihar Kano.
Dr. Nuraddeen!-->!-->!-->…
Gamayyar Marassa Rinjaye A Majalissar Wakilai Ta Nemi A Gaggauta Janye Ƙarin Farashin Mai
Gamayyar marassa rinjaye a Majalisar Wakilai ta nemi a gaggauta janye ƙarin farashin man fetur da aka ƙara kwanan nan, saboda hakan zai ƙara wa 'yan Najeriya wahala.
Sanarwar da shugabansu Kingsley Chinda ya fitar ta ce wannan ƙarin!-->!-->!-->…
Kano Pillars Ta Sanyan Hannu Kan Ɗaukar Sababbin Ƴan Wasa 12, Ta Kuma Riƙe Ƴan Wasa 20 Gabanin Kakar…
Tawagar Kano Pillars FC, wacce ta lashe gasar Nigeria Premier Football League, NPFL, sau hudu, ta sanar da sababbin ‘yan wasan da ta dauka a hukumance gabanin kakar wasanni ta 2024/25.
An gudanar da taron bikin bayyana ‘yan wasan a!-->!-->!-->…
YANZU-YANZU: Ɗaliban Najeriya Zasu Rufe Duk Manyan Birane, Yayin Da NANS Ta Ba Da Sanarwar Fara…
Kungiyar Daliban Najeriya, NANS, ta fitar da sanarwar shirin rufe dukkan manyan biranen Najeriya, daga ranar 15 ga Satumba, 2024.
Zanga-zangar na da nufin nuna rashin amincewa da ƙarin farashin man fetur da kuma zargin rashin kwarewa da!-->!-->!-->…
Kotun Amurka Ta Ɗaure Ƴan Najeriya Kan Laifin Damfarar Dala Miliyan 5
Wata Kotun Tarayya a Amurka ta yanke wa wasu ‘yan Najeriya biyu, Franklin Okwonna da Ebuka Umeti, hukuncin zaman gidan yari bisa laifin da suka aikata na damfara ta intanet da ta yaudari mutane sama da dala miliyan $5.
Wannan bayani ya!-->!-->!-->…
Adadin Karɓar Rigakafi Ya Ƙaru Zuwa Kashi 49% Cikin Shekara Biyar A Jigawa – Hukuma
Daraktan Kiwon Lafiya a Matakin Farko na Jihar Jigawa, Dr. Shehu Sambo, ya ce adadin rigakafi ya karu daga kashi bakwai cikin dari a shekarar 2016 zuwa kashi 49 cikin dari a shekarar 2021.
Sambo ya bayyana hakan ne yau Laraba a Dutse,!-->!-->!-->…
Gwamnatin Jigawa Za Ta Kafa Cibiyoyin Kula Da Ciwon Ƙoda Biyar A Jihar
Gwamnatin Jihar Jigawa ta shirya kafa cibiyoyin kula da ciwon ƙoda guda biyar a jihar, kamar yanda Kwamishinan Lafiya, Dr. Muhammed Kainuwa ya bayyana.
Kainuwa ya bayyana hakan ne a Dutse yayin buɗe taron karɓar takardun neman kwangilar!-->!-->!-->…
Kwalara Ta Yi Ajalin Mutane 7 A Jigawa
Daga: Lukman Dahiru
An samu ɓarkewar cutar amai da gudawa a Ƙaramar Hukumar Kirikasamma ta Jihar Jigawa, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai, yayin da aka kwantar da wasu da dama a asibiti.
Shugaban kula da lafiyar al’umma!-->!-->!-->!-->!-->…
Yawan Wutar Lantarki Ya Kai Megawatt 5,313, Karo na Farko Cikin Shekaru 3 – Minista
Yawan wutar lantarki a Najeriya ya karu zuwa megawatt 5,313 a ranar Litinin da ta gabata, karo na farko cikin shekaru uku, a cewar Ma’aikatar Wutar Lantarki.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bolaji Tunji, Mai ba da shawara ta!-->!-->!-->…
Fursunoni 3,590 Na Jiran Hukuncin Kisa A Najeriya – NCoS
Akalla fursunoni 3,590 ne da ke cikin gidajen gyaran hali a fadin Najeriya ke jiran hukuncin kisa, kamar yanda Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) ta bayyana.
Mai magana da yawun hukumar, Mataimakin ACC Abubakar Umar,!-->!-->!-->…
NNPCL: NLC Ta Kira Zaman Gaggawa Kan Ƙarin Farashin Fetur
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC, ta bayyana shirinta na yin zaman gaggawa dangane da karin kashi 45 cikin 100 a farashin man fetur da Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPCL, ya yi kwanan nan.
Wannan na zuwa ne yayin da ƙungiyar ta!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Kakkaɓe Ƴanbindiga Yayin Da Minista, CDS Suka Isa Sokoto
A jiya ne Gwamnatin Tarayya ta bakin Ƙaramin Ministan Tsaro, Dr. Bello Matawalle, ta sha alwashin kakkaɓe ƴanbindiga da sauran gungun masu aikata laifuka da ke addabar yankin arewa maso yamma, biyo bayan umarnin Shugaban Kasa Bola Tinubu!-->…
HAUHAWAR FARASHI: FCCPC Ta Janye Shirinta Na Daidaita Farashin Kayayyaki A Najeriya
Biyo bayan cece-kuce da aka samu game da barazanar da Hukumar Kula da Gasar Kasuwanci da Kare Haƙƙin Masu Sayen Kaya ta Kasa (FCCPC) ta yi na shiga tsakani kan hauhawar farashin kayayyaki, hukumar ta bayyana cewa ba za ta shiga cikin!-->…
NLC Ta Yi Watsi Da Ƙarin Kuɗin Man Fetur, Ta Ce Gwamnati Ta Saɓa Alƙawarin Da Aka Yi Da Ita
Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta ce ƙarin farashin fetur da aka yi kwanan nan abin firgici ne da tayar da hankali.
NLC ta kuma ce Gwamnatin Tarayya ta yi mata kafar ungulu bayan yarjejeniyar da suka cimma yayin tattaunawa kan mafi!-->!-->!-->…