Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
News
Najeriya Na Neman Sabon Bashin Naira Tiriliyan 1.2 Da Wasu Basussukan Daga Bankin Duniya
A yanzu haka Gwamnatin Tarayya na tattaunawa da Bankin Duniya kan sabon bashin da ya kai dalar Amurka biliyan 1.5 daidai da naira Tiriliyan 1.2, kamar yanda jaridar PUNCH ta gano.
Gwamnatin na neman bashin ne da a kai wa take da HOPE!-->!-->!-->…
Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Gwamnan Bauchi Ta Tabbatar Da Nasarar Bala Mohammed
Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Gwamnan Bauchi ta kori ƙarar da jam’iyyar APC da ɗan takararta na gwamna Sadique Abubakar su ka shigar su na ƙalubalantar nasarar da Bala Mohammed na jam’iyyar PDP ya samu a zaɓen gwamnan Jihar Bauchi na!-->…
YANZU-YANZU: Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Ƙwace Nasarar Abba Gida-Gida Ta Bai Wa Gawuna Kano
Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe ta Zaɓen Gwamnan Kano ta soke nasarar da Abba Kabir Yusuf ya samu a zaɓen gwamnan Kano na ranar 18 ga watan Maris saboda aringizon ƙuri’u, inda ta bayyana Nasir Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda!-->…
Tinubu Ya Naɗa Hakeem Baba Ahmed A Matsayin Mai Bayar Da Shawara Na Musamman
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Mai Magana da Yawun Ƙungiyar Dattawan Arewa, Dr. Hakeem Baba-Ahmed a matsayin Mai Bayar da Shawara na Musamman a Kan Harkokin Siyasa a Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.
Baba-Ahmed!-->!-->!-->…
Tinubu Ya Naɗa Madadin Garba Shehu Da Wasu Muƙaman Da Dama
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa tshohon Babban Manaja kuma Editan Jaridar Leadership, Kingsley Stanley Nkwocha, a matsayin Babban Mai Temakawa Shugaban Ƙasa, SSA a ɓangaren Kafafen Yaɗa Labarai da Sadarwa.
Shugaban ya naɗa!-->!-->!-->…
Gwamnan Jigawa Ya Gargaɗi JSIEC Da Ta Bayar Da Dama Ga Duk Jam’iyyu A Zaɓen Ƙananan Hukumomin Da Ke…
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya gargaɗi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Jigawa, JSIEC da ta bayar da dama ga kowacce jam’iyya a zaɓuɓɓukan ƙananan hukumomi da ke tafe a jihar.
Wannan na ƙunshe ne cikin takardar sabunta!-->!-->!-->…
Gwamnatin Jigawa Za Ta Kafa Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci, Yayin Da Fursunoni 1,576 Cikin 1,718 A Jihar…
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce, akwai matasa ƴan fursuna guda dubu 1,576 da ke zaman gidajen yari a jihar cikin fursunoni dubu 1,718 da ake da su a gidajen yarin jihar.
Kwamishinan Shari’a na Jihar, Barrista Dr. Musa Adamu Aliyu ne ya!-->!-->!-->…
YAJIN AIKI: Yayin Da NLC Ke Shirin Tsunduma Yajin Aiki, Gwamnatin Tarayya Ta Gayyace Ta Zaman…
Gwamnatin Tarayya ta kuma gayyatar shugabancin Ƙungiyar Ƴan Ƙawadago, NLC, zuwa wajen zaman tattaunawa domin magance matsalolin da za su sa ƙungiyar shiga yajin aiki.
An tsara cewar za a gudanar da zaman ne tsakanin ɓangarorin biyu a!-->!-->!-->…
Gwamnatin Kano Za Ta Raba Littattafai Miliyan 3 A Makarantu, Za Ta Kuma Ginawa Malamai Gidaje
Gwamnatin Jihar Kano za ta raba littattafai miliyan uku ga ɗaliban da su ke karatu a makarantun gwamnati da ke jihar.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Umar Haruna Doguwa ne ya bayyana hakan a yau, yayin shirin BBC Hausa na ‘A Faɗa A!-->!-->!-->…
An Damfara Tinubu A Kotu Kan Ƙin Hana Badaru Da Wasu Tsofin Gwamnoni Karɓar Fansho
Ƙungiyar Tabbatar da Gaskiya da Kare Haƙƙin Al’umma a Zamantakewa da Tattalin Arziki ta SERAP ta shigar da ƙarar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan gazawarsa na dakatar da tsofin gwamnonin da ya naɗa ministoci daga karɓar fansho da sauran!-->…
YANZU-YANZU: Tinubu Ya Naɗa Jamila Da Ayodele A Matsayin Ministocin Matasa
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Dr. Jamila Bio Ibrahim da Mr. Ayodele Olawande a matsayin ministocin da za su jagoranci Ma’aikatar Matasa ta Tarayya.
Sanarwar naɗin na su ta fito ne a wani jawabi da Mai Bayar da Shawara na!-->!-->!-->…
Tinubu Ya Karya Dokar CBN Wajen Naɗa Madadin Emefiele, In Ji Wani Lauya
Babban Daraktan Ƙungiyar Wayar da Kan Ƴan Ƙasa kan Ƴancin Kai ta CASER, Frank Tietie ya ƙalubalanci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa karya dokar Babban Bankin Najeriya, CBN kan cire tsohon gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele, tsofin!-->…
JERIN SANAYE: Gwamnati Ta Goge Baragurbin Apps Na Bayar Da Bashi
Adadin apps na bayar da bashi da aka goge ya ƙaru daga tara zuwa 37, kamar yanda Hukumar Kula da Haƙƙin Mai Saye da Gogayya Tsakanin Kasuwanci ta Tarayya, FCCPC, ta fitar.
Haka kuma adadin apps na bayar da bashi waɗanda gwamnati ta!-->!-->!-->…
YANZU-YANZU: Sanannen Malamin Musulunci Gero Argungu Ya Rasu
Al’ummar Musulmai a Najeriya na jimamin rasuwar sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Gero Argungu wanda ya rasu a asibitin Birnin Kudu a yau Laraba.
Shugaban Ƙungiyar Izala na Ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana a!-->!-->!-->…
Kotun Zaɓe Ta Tabbatar Da Nasarar Tinubu, Ta Ce Masu Ƙalubalantarsa Sun Rasa Hujjoji
Kutun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa a yau Laraba ta yanke hukuncin cewar, waɗanda su ke ƙalubalantar zaɓen shugaban ƙasa, sun gaza gabatar da hujjojin da ke nuni da cewar akwai kuskure a bayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda!-->…
DSS Ta Kama Jami’in Gwamnati Da Karkatar Da Kayan Tallafin Rage Raɗaɗi
Rundunar Tsaro ta Farin Kaya, DSS, ta kama wani ma’aikacin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Nasarawa da wasu mutane da yake aiki da su, bisa zargin karkatar da kayan tallafin da aka tanadarwa talakawan da ke cikin matsatsi.
Ana!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: A Ƙarshe Dai NNPP Ta Kori Kwankwaso Saboda Yi Wa Jam’iyyar Zagon Ƙasa
Tsagin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ƙarƙashin shugabancin Major Agbo ta kori ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen da ya gabata, Sanata Rabiu Kwankwaso saboda zargin aikata zagon ƙasa ga jam’iyyar da kuma badaƙalar!-->…
Gaskiyar Dalilina Na Zaɓar Ƴar’adua Ya Zama Shugaban Ƙasa – Obasanjo
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo ya ce, ya zaɓi marigayi Shugaban Ƙasa Umaru Musa Ƴar’adua ya gaje shi duk da ya san cewar ba shi da lafiya.
Ya ce, ya ɗau hukuncin ne saboda shawarar masana lafiya da ta nuna cewar, Ƴar’adua wanda!-->!-->!-->…
Tinubu Ya Ce Yana Firgita In Aka Nuna Ma Sa Yawan Ma’aikatan Da Ke Karɓar Albashi A Najeriya
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwarsa bisa yawan ma’aikatan da ke karɓar albashi a matakin ƙasa da sauran matakai.
Shugaban Ƙasar ya bayyana abin da ke zuciyarsa ne a jiya Litinin lokacin da ya ke magana a wajen wani zaman!-->!-->!-->…
Kwamitin Majalissar Wakilai Ya Dakatar Da Aikinsa Saboda Yajin Aikin NLC
Saboda yajin aikin gargaɗin da NLC ta sanar da farawa a yau, kwamitin wucin gadi da ke bincikar badaƙalar ɗaukar ma’aikata a ma’aikatu da hukumomi, a jiya Litinin ya sanar da ɗage ci gaba da aikinsa har sai ranar Alhamis 7 ga watan!-->…