Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
News
An Damƙe Mai Yin Takin Zamanin Bogi, Yana Sawa A Buhun Takin Zamanin Gaske
Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki ta Najeriya, SON, a Jihar Bauchi ta ce, jami’anta sun damƙe wani mai sarrafa takin zamanin bogi a garin Chinade da ke Ƙaramar Hukumar Katagum ta jihar.
Hukumar ta kuma ce, ta samu nasarar ƙwace aƙalla!-->!-->!-->…
JANYE TALLAFI: Jihohin Borno, Adamawa Da Yobe Sun Sauƙaƙawa Ma’aikata, Manoma Da Ɗalibai Kuɗin Hawa…
Gwamnatocin jihohin Borno, Adamawa da Yobe sun fara ɗaukar matakan rage raɗaɗin tsadar kuɗin mota da ya samo asali daga janye tallafin mai da Gwamnatin Tarayya ta yi.
Kamfanin Dillanci Labarai na Najeriya, NAN, ya rawaito cewa,!-->!-->!-->…
Wani Gwamna Ya Amince Da A Ɗebi Sabbin Malaman Makaranta A Jiharsa
Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya amince da a ɗebi malaman firamare, ƙananan ma’aikatan ofis da masu gadi a ƙananan hukumomi 22 na jihar.
Shugaban Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi ta Najeriya, ALGON reshen Jihar Delta, Victor Ebonka!-->!-->!-->…
Za A Iya Gyara Rayuwa A Ci Ribarta Ta Hanyar Lura Da Abubuwa Biyar
Daga: Aliyu M Ahmad
Idan kana karanta rubutun nan, ɗauko biro da takarda, ko ka buɗe 'WPS' ko wani 'word processor app', ko 'notepad' na wayarka:
1. Ka tracking na routines dinka, daga asuba zuwa dare lokacin da kake shirin bacci, me!-->!-->!-->!-->!-->…
Ƴan Najeriya Miliyan 19 Ne Ke Fama Da Ciwon Hanta
Shugaban Shirin Kula da Cututtukan AIDS da STDs na Ƙasa, Dr. Adebobola Bashorun ya ce, a ƙalla mutane miliyan 19 ne ke fama da ciwon hanta a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne jiya Juma’a a Abuja lokacin da yake jawabi ga mahalarta taron da!-->!-->!-->…
Ma’aikatan Lafiya Zasu Shiga Yajin Aikin Da NLC Ta Shirya Shiga Ranar Laraba
Ma’aikatan lafiya ƙarƙashin Haɗakar Ƙungiyoyin Ma’aikatan Lafiya, JOHESU, da Ƙungiyar Ma’aikatn Jiyya da Ungozoma ta Ƙasa sun ce zasu shiga yajin aikin da Ƙungiyar Ƙwadago, NLC ta shirya shiga a ranar Laraba, 2 ga watan Agusta mai zuwa.
!-->!-->!-->…
Tinubu Zai Haɗe, Raba, Ruguje Da Ƙirƙirar Wasu Ma’aikatun A Gwamnatin Tarayya
Biyo bayan gabatar da rukuni na farko na waɗanda shugaban ƙasa ke son naɗawa ministoci, alamu sun nuna cewa, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai sake fasalin wasu ma’aikatun Gwamnatin Tarayya ta hanyar haɗe wasu, ƙirƙirar wasu da!-->…
Dangi 5 Mafiya Kuɗi A Duniya
Daga: Kabiru Zubairu Birnin Kudu
Tattalin arziƙi da mallakar dukiya a duniya na fuskantar matsaloli a ƴan shekarun nan saboda lalacewar tattalin arziƙin duniya. Masu arziƙi da dama sun yi asara, wasu ma sun karye. Mallakar dukiya a!-->!-->!-->…
Sojoji Sun Kashe Ƴanta’adda 59, Sun Kama 88
Rundunar Sojojin Najeriya ta tabbatar da kashe aƙalla ƴanta’adda 59 tare da kama wasu 88, sannan kuma sojojin sun samu nasarar kama masu garkuwa da mutane 10 da adadi mai yawa na masu satar ɗanyen mai.
Mai Magana da Yawan Rundunar!-->!-->!-->…
Cikakken Bayani Kan Sabon Shugaban Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani
A wuni na biyu bayan sojoji sun bayyana cewa sun kifar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum, Janar Abdourahmane Tchiani (wanda ake kira Omar Tchiani) ya bayyana a kafar talabijin inda ya yi wa al'umma jawabi.
Ta tabbata cewa shi ne sabon!-->!-->!-->…
Wani Mutum Ya Mutu Yayinda Yake Gujewa Kare
Wani mutum da aka bayyana sunansa da Mohammed Faworaja ya gamu da ajalinsa a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara a lokacin da yake gujewa kare.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne a kusa Asa Dam da ke yankin Warah-Osin a!-->!-->!-->…
Ɗan Majalissar Jigawa Mai Wakiltar Birnin Kudu Zai Nemawa Matasa Guraben Karatu
Ɗan Majalissar Jihar Jigawa mai wakilatar Mazaɓar Birnin Kudu, Muhammad Kabir Ibrahim ya yi alƙawarin nemawa matasan mazaɓarsa guraben karatu a Kwalejin Horar da Malamai ta Jihar Jigawa da ke Gumel.
Ɗan Majalissar ya bayyana hakan ne a!-->!-->!-->…
Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Ƴanmata Da Zawarawa 23 A Zamfara
Wasu ƴanbindiga da ake zargin ƴan ta’adda ne sun yi garkuwa da mata ashirin da uku a garin Damaga na Ƙaramar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara.
Wani mazaunin yankin, Malam Ahmed Mohammed ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da DAILY POST!-->!-->!-->…
El-Rufa’i Zai Haɗa Faɗa Tsakanin Tinubu Da Shettima – Shehu Sani
Babban ɗan jam’iyyar PDP, Sanata Shehu Sani ya yi hasashen cewa, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i zai iya jawo rigima tsakanin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima
Da yake magana a!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya Ta Ce A Dinga Amfani Da Harsunan Uwa A Koyarwa
A jiya Alhamis ne wani babban jami’in Ma’aikatar Ilimi ya ce, Gwamnatin Tarayya za ta inganta amfani da harsunan uwa wajen koyarwa, musamman a a makarantun firamare da ƙaramar sikandire.
Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi, David Adejo ne!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙara Alawuns Na Hazard Ga Wasu Ma’aikata
Gwamnatin Tarayya ta amince da ƙarin alawuns na hazard ga ma’aikatan lafiya da ba na asibitoci ba a fadin ƙasar nan.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a sanarwar da ta raba mai ɗauke da kwanan watan 26 ga Yuli, 2023, wadda Shugaban Hukumar!-->!-->!-->…
CAC Zata Goge Kamfanoni Dubu 100 Daga Kamfanonin Da Taiwa Rijista
Hukumar Kula da Kamfanoni, CAC, ta ce zata cire kamfanoni 100,000 daga jerin kamfanonin da suke da rijista a Najeriya nan ba da jimawa ba.
A wajen taron horaswa kan amfanuwa da rijistar mallaka a Lagos, Shugaban Hukumar CAC, Alhaji!-->!-->!-->…
Next Jigawa Ta Yi Kira Ga Gwamnatin Jihar Da Ta Ɗebi Ƙarin Ma’aikata
Ƙungiyar ci gaban al’umma ta Next Jigawa ta yi kira ga gwamnatin jihar da cire takunkumi kan ɗiban ma’aikata tare ɗiban ma’aikatan da zasu cike guraben aikin da ake da su a jihar.
Shugaban Ƙungiyar, Farfesa Haruna Usman ne ya yi kiran,!-->!-->!-->…
Ɗan El-Rufa’i Da Ƴar Ibori Sun Sami Shugabanci A Yayin Majalissar Wakilai Ta Fitar Kwamitoci
Mohammed Bello El-Rufai, ɗan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i da Erhiatake Ibori-Suenu, ƴar tsohon Gwamnan Jihar Delta, James Ibori sun sami shugabancin kwamitocin dindindin na Majalissar Wakilai a yau Thursday.
!-->!-->!-->…
Sama Da Ƴan Afirka Miliyan 300 Ne Ke Kwana Da Yunwa A Kullum
Bankin Fitarwa da Shigarwa da Kayayyaki na Afirka, Afrixembank ya ce, sama da ƴan Afirka miliyan 300 ne ke kwana da yunwa a kullum.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya bayyana cewa, Shugaban Daraktocin Bankin Afreximbank, Dr.!-->!-->!-->…