Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Top News
Talauci A Najeriya Zai Zarce Hasashen Bankin Duniya Kwanan Nan Saboda Tsadar Man Fetur
Masana tattalin arziƙi sun yi gargaɗin cewa adadin ƴan Najeriya da ke ƙasa da layin talauci na iya zarce hasashen Bankin Duniya na mutane miliyan 104, sakamakon hauhawar farashin fetur da matsalolin samar da abinci da ƙasar ke fuskanta.
!-->!-->!-->…
Mun Fi Son A Rage Tsadar Kuɗin Makaranta Maimakon A Bamu Bashi – Ɗalibai Ga Gwamnati
Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya (NANS) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta rage tsadar kuɗin karatu maimakon samar da tsarin bashi ga ɗalibai.
Shugaban Ƙungiyar, Henry Okuomo ne ya bayyana hakan a jiya Juma’a, a wata hira da aka yi da shi a!-->!-->!-->…
BASHIN KARATU: Mun Fara Jin Alat Na Kuɗin Rijistar Ɗalibanmu – Shugaban Wata Makaranta
Shugaban makarantar Moshood Abiola Polytechnic, MAPOLY, da ke Abeokuta, Dr. Adeoye Odedeji, ya ce ɗaliban makarantar sun fara samun kuɗi na bashin karatun da suka nema.
Odedeji ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a Abeokuta yayin rantsar!-->!-->!-->…
Ku Kare Kanku Daga Ƴanta’add, Gwamnan Katsina Ya Shawarci Ƴan Jiharsa
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya yi kira ga al’ummar jihar da su ɗauki matakan kariya don kare kansu daga hare-haren ƴanbindiga da ke addabar jihar.
Ya bayyana hakan ne a taron dandalin tattaunawa da aka gudanar mai taken:!-->!-->!-->…
Mutane 13, 346 Aka Kashe, Aka Sace 9,207 A Watanni 16 Na Mulkin Tinubu, In Ji Wani Rahoto
Tun bayan rantsar da Shugaba Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, Najeriya ta fuskanci ƙaruwar tashin hankali, inda aka kashe mutane 13,346 aka kuma yi garkuwa da 9,207 a fadin kasar.
Wannan ƙaruwar tashin hankalin da ta shafi!-->!-->!-->…
Tinubu Na Ƙoƙarin Ɗabbaƙa Cigaban Ababen More Rayuwa Irin Na China A Najeriya
Shugaban kasa Bola Tinubu ya nuna kudirinsa na kwaikwayon cigaban kasar Sin a fannin ababen more rayuwa a Najeriya bayan ziyararsa zuwa kasar.
Ya bayyana hakan ne yayin ganawa da kungiyar 'yan Najeriya mazauna kasar Sin (NIDO China) da!-->!-->!-->…
Ba Mu Hana Ƴan Ƙasa Da Shekara 18 Rubuta WASSCE Da NECO Ba – Ministan Ilimi
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta fayyace cewa ba ta dakatar da ɗaliban da ba su kai shekara 18 ba daga rubuta jarrabawar WASSCE ko NECO.
Ƙaramin Ministan Ilimi, Dr. Yusuf Sununu ne ya bayyana haka a Abuja yayin da yake amsa tambayoyi daga!-->!-->!-->…
A Shirye Nake Na Ɗau Duk Wasu Tsauraran Matakai Don Ciyar Da Najeriya Gaba – Tinubu
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa yana shirye ya ɗauki tsauraran matakai don ciyar da ƙasa gaba, duk da cewa ba koyaushe ake samun haɗin kan ƴan ƙasa kan batutuwan ba.
Tinubu ya yi wannan bayani ne a Beijing lokacin da yake!-->!-->!-->…
NANS Ta Roƙi Gwamnati Da Ta Janye Sokewar Da Tai Wa Digirin Benin Da Togo
Shugabannin Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya ta NANS a yankin kudu maso yamma sun roƙi gwamnatin tarayya da ta sake nazari kan soke shaidar karatun digiri daga manyan makarantu na ƙasar Benin da Togo.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Reshen!-->!-->!-->…
Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 152, Sun Kama 109, Sun Ceto Mutane 91
Sojoji sun kashe ƴan ta’adda 152, sun kama 109, sun ceto mutane 91 da aka yi garkuwa da su, a yayin da suke yaƙi da matsalar tsaro a fadin kasar nan cikin makon da ya gabata.
Sojojin sun kai hari kan sansanonin wasu manyan shugabannin!-->!-->!-->…
Yanda Ƴanbindiga Suka Ciyar Da Karnukansu Naman Direban Ƴan’uwana – Wani Malami A Sokoto
Sheikh Bashar Danfili, wani sannanen malami a Jihar Sokoto, ya nemi taimakon kudi daga jama’a bayan ƴan bindiga sun sace ƴan’uwansa guda shida a hanyarsu zuwa wani ƙauye a jihar.
Ya bayyana hakan ne a cikin wani gajeren bidiyo da ya!-->!-->!-->…
Kukah Ya Roƙi Shugabannin APC Da Su Janye Ƙarin Kuɗin Man Fetur A Kan Ƴan Najeriya
Bishop Mathew Hassan Kukah na Cocin Katolika ta Sokoto ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar APC mai mulki da su rage farashin man fetur da ake sayarwa, yana mai cewa ƴan Najeriya na cikin halin yunwa.
Ya yi wannan jawabi ne a yau Juma'a!-->!-->!-->…
Ƴanta’adda Sun Mayar Mu Bayi, Suna Sa Mu Aiki A Gonakinsu – Ƴan Jihar Niger
Mutanen da ke zaune a wasu garuruwa da ke fama da matsalar tsaro a Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja, sun koka cewa ƴan ta’adda da ƴan bindiga na bautar da su wajen aikin gona a gonakin su.
An gano cewar, shugaban wata ƙungiyar!-->!-->!-->…
CAC Ta Gargaɗi Masu POS Da Ba Su Yi Rijista Ba, Ta Ce Ana Iya Rufe Asusunsu
Hukumar CAC ta gargadi masu gudanar da kasuwancin POS da ba su yi rijista ba yayin da wa’adin da aka ba su ya ƙare.
Tun a baya dai aka sanar da su wa’adin yin rijista da aka ayyana tun ranar 7 ga Yuli, 2024, kuma wa’adin ya cika a ranar!-->!-->!-->…
Iya Masu NIN Number Ne Zasu Mori Sayen Shinkafa Kan Farashin Naira 40,000
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kawai mutanen da ke da Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa ta NIN ne za su samu damar sayen buhun shinkafa mai nauyin 50kg a farashin N40, 000 a matsayin wani bangare na tallafin abinci ga ƴan Najeriya.
Shugaban!-->!-->!-->…
Sai Ranar 15 Ga Satumba Man Ɗangote Zai Shiga Gidajen Man Najeriya – NNPC
Matatar Man Fetur ta Dangote zata fara cika kasuwar man fetur da mai daga ranar 15 ga Satumba, 2024, kamar yanda Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPCL, ya sanar.
Sanarwar da Olufemi Soneye, Jami’in Hulda da Jama’a na NNPCL ya!-->!-->!-->…
Ƴanbindiga Sun Kama Mutum 22 A Wani Sabon Hari A Kaduna
A wasu hare-hare daban-daban da aka kai, ƴan bindiga sun sace mutum 19 a unguwar Mani kusa da wani kamfani a Mazaɓar Rido da ke Ƙaramar Hukumar Chikun da kuma yankin Danhonu II Millennium City a Kaduna.
A garin na Mani, ƴan bindigar sun!-->!-->!-->…
Wasu Fitattun Mutane Sun Zama Shugabannin Ƙungiyar One Voice Development Initiative
Ƙungiyar One Voice Development Initiative ke da muradin inganta shugabanci na gari, nuna gaskiya a harkokin jama'a, da ci gaban siyasa, ta sanar da sabbin shugabanninta na ƙasa.
Abbas Abdullahi, CISSP, IPMA, ne ya zama shugaban ƙungiyar!-->!-->!-->…
Ƴan Najeriya 9 Da Aka Tabbatar Da Sunayensu Don Karɓar Kyautar Ballon d’Or
Kyautar Ballon d'Or ce mafi girman nasarar kowane ɗan wasan ƙwallon ƙafa, wadda ake bayarwa duk shekara ga mafi kyawun 'yan wasa mata da maza a duniya.
Tun daga kafuwarta a shekarar 1956, ta zama alamar babbar lambar yabo da kowane ɗan!-->!-->!-->…
YANZUNNAN: Mutum 2 Sun Mutu, 2 Sun Jikkata A Rugujewar Gini A Kano
Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane biyu da jikkatar wasu biyu a lokacin da wani bene mai hawa biyu ya rufta a unguwar Noman’s Land, da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a Jihar Kano.
Dr. Nuraddeen!-->!-->!-->…