Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Top News
Gwamnatin Kano Za Ta Raba Littattafai Miliyan 3 A Makarantu, Za Ta Kuma Ginawa Malamai Gidaje
Gwamnatin Jihar Kano za ta raba littattafai miliyan uku ga ɗaliban da su ke karatu a makarantun gwamnati da ke jihar.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Umar Haruna Doguwa ne ya bayyana hakan a yau, yayin shirin BBC Hausa na ‘A Faɗa A!-->!-->!-->…
An Damfara Tinubu A Kotu Kan Ƙin Hana Badaru Da Wasu Tsofin Gwamnoni Karɓar Fansho
Ƙungiyar Tabbatar da Gaskiya da Kare Haƙƙin Al’umma a Zamantakewa da Tattalin Arziki ta SERAP ta shigar da ƙarar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan gazawarsa na dakatar da tsofin gwamnonin da ya naɗa ministoci daga karɓar fansho da sauran!-->…
YANZU-YANZU: Tinubu Ya Naɗa Jamila Da Ayodele A Matsayin Ministocin Matasa
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Dr. Jamila Bio Ibrahim da Mr. Ayodele Olawande a matsayin ministocin da za su jagoranci Ma’aikatar Matasa ta Tarayya.
Sanarwar naɗin na su ta fito ne a wani jawabi da Mai Bayar da Shawara na!-->!-->!-->…
Tinubu Ya Karya Dokar CBN Wajen Naɗa Madadin Emefiele, In Ji Wani Lauya
Babban Daraktan Ƙungiyar Wayar da Kan Ƴan Ƙasa kan Ƴancin Kai ta CASER, Frank Tietie ya ƙalubalanci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa karya dokar Babban Bankin Najeriya, CBN kan cire tsohon gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele, tsofin!-->…
JERIN SANAYE: Gwamnati Ta Goge Baragurbin Apps Na Bayar Da Bashi
Adadin apps na bayar da bashi da aka goge ya ƙaru daga tara zuwa 37, kamar yanda Hukumar Kula da Haƙƙin Mai Saye da Gogayya Tsakanin Kasuwanci ta Tarayya, FCCPC, ta fitar.
Haka kuma adadin apps na bayar da bashi waɗanda gwamnati ta!-->!-->!-->…
YANZU-YANZU: Sanannen Malamin Musulunci Gero Argungu Ya Rasu
Al’ummar Musulmai a Najeriya na jimamin rasuwar sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Gero Argungu wanda ya rasu a asibitin Birnin Kudu a yau Laraba.
Shugaban Ƙungiyar Izala na Ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana a!-->!-->!-->…
Kotun Zaɓe Ta Tabbatar Da Nasarar Tinubu, Ta Ce Masu Ƙalubalantarsa Sun Rasa Hujjoji
Kutun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa a yau Laraba ta yanke hukuncin cewar, waɗanda su ke ƙalubalantar zaɓen shugaban ƙasa, sun gaza gabatar da hujjojin da ke nuni da cewar akwai kuskure a bayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda!-->…
DSS Ta Kama Jami’in Gwamnati Da Karkatar Da Kayan Tallafin Rage Raɗaɗi
Rundunar Tsaro ta Farin Kaya, DSS, ta kama wani ma’aikacin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Nasarawa da wasu mutane da yake aiki da su, bisa zargin karkatar da kayan tallafin da aka tanadarwa talakawan da ke cikin matsatsi.
Ana!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: A Ƙarshe Dai NNPP Ta Kori Kwankwaso Saboda Yi Wa Jam’iyyar Zagon Ƙasa
Tsagin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ƙarƙashin shugabancin Major Agbo ta kori ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen da ya gabata, Sanata Rabiu Kwankwaso saboda zargin aikata zagon ƙasa ga jam’iyyar da kuma badaƙalar!-->…
Gaskiyar Dalilina Na Zaɓar Ƴar’adua Ya Zama Shugaban Ƙasa – Obasanjo
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo ya ce, ya zaɓi marigayi Shugaban Ƙasa Umaru Musa Ƴar’adua ya gaje shi duk da ya san cewar ba shi da lafiya.
Ya ce, ya ɗau hukuncin ne saboda shawarar masana lafiya da ta nuna cewar, Ƴar’adua wanda!-->!-->!-->…
Tinubu Ya Ce Yana Firgita In Aka Nuna Ma Sa Yawan Ma’aikatan Da Ke Karɓar Albashi A Najeriya
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwarsa bisa yawan ma’aikatan da ke karɓar albashi a matakin ƙasa da sauran matakai.
Shugaban Ƙasar ya bayyana abin da ke zuciyarsa ne a jiya Litinin lokacin da ya ke magana a wajen wani zaman!-->!-->!-->…
Kwamitin Majalissar Wakilai Ya Dakatar Da Aikinsa Saboda Yajin Aikin NLC
Saboda yajin aikin gargaɗin da NLC ta sanar da farawa a yau, kwamitin wucin gadi da ke bincikar badaƙalar ɗaukar ma’aikata a ma’aikatu da hukumomi, a jiya Litinin ya sanar da ɗage ci gaba da aikinsa har sai ranar Alhamis 7 ga watan!-->…
ASUU, ASUP, Bankuna Da Ma’aikatan Wutar Lantarki Sun Shiga Yajin Aiki Ƙarƙashin NLC
Ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC, sun jaddada goyon bayansu na shiga yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyu da NLC ta fara a yau Talata.
Ƙungiyoyin sun haɗa da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU; Ƙungiyar!-->!-->!-->…
NLC Ta Ƙi Yarda Da Kiran Gwamnatin Tarayya, Ta Jaddada Shiga Yajin Aiki
Shugabancin Ƙungiyar Ƙwadago, NLC, ya bijirewa zaman da Ministan Ƙwadago da Ɗaukar Ma’aikata, Simon Lalong ya kira domin dakatar da yajin aikin kwanaki biyu da NLC ta fara a yau Talata.
A zaman da aka gudanar jiya Litinin da yamma, iya!-->!-->!-->…
Kira Ga Gwamna Ɗanmoɗi Kan Gyaran Matsalar APC A Birnin Kudu
Daga: Abubakar Ibrahim Ayuba (Habu Maja)
Ba abu ne ɓoyayye ba cewar akwai gagarumar matsala a jam’iyyarmu ta APC a Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu. Za a iya tabbatar da haka idan aka yi la’akari da irin ƙarfin da muke da shi lokacin da muka!-->!-->!-->…
NNPP Za Ta Binciki Kwankwaso Kan Zargin Badaƙalar Sama Da Naira Miliyan Dubu Na Jam’iyya
Ɗaya daga cikin tsagin jami’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ƙarƙashin jagorancin Major Agbo, ya sanar da cewar zai binciki ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen da ya gabata, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da wasu makusantansa!-->…
Ɗalibai Da Fusatattun Matasa Na Shirin Yin Zanga-Zangar Tarzoma Kan Matsatsin Da Ake Ciki A…
Sashin Tsaro na Farin Kaya, DSS, a yau Litinin ya bayyana cewar ya gano shirin da wasu suke yi a sassan ƙasar nan da gudanar da zanga-zanga mai ɗauke da tarzoma.
A sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na DSS, Peter Afunanya ya fitar, ya!-->!-->!-->…
Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Dawo Da Dukkan Ambasadojin Najeriya Gida
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo dukkan ambasadojin Najeriya da ke ƙasashe daban-daban gida, in ji Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje.
Wannan na cikin sanarwar da Mai Taimakawa na Musamman kan Harkokin Sadarwa da Yaɗa Labarai na!-->!-->!-->…
YANZU-YANZU: Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Gidajen El-Rufai A Abuja, Sun Tafi Da Wani Magidanci
Mazauna unguwar Kuchiko Resettlement Development Area (KRDA) da ke unguwar Bwari a Abuja sun sanar da yawaitar garkuwa da mutanen da ake yi a unguwar.
Wannan ya biyo bayan lamarin da ya faru da sanyin safiyar yau Asabar, a unguwar da!-->!-->!-->…
Gwamnan Kano Ya Naɗa Ƙarin Masu Ba Shi Sahawara Guda 14 Da Masu Ba Shi Rahoto Guda 44
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a yau Asabar hya sanar da ƙarin wasu masu ba shi shawara da ya naɗa su 14 da kuma manyan masu ba shi rahoto daga ma’aikatu da hukumomi a jihar su 44.
Wannan sanarwar na ƙunshe ne cikin snarwar da!-->!-->!-->…