Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Top News
Adadin Wadanda Suka Mutu Sanadiyyar Rikicin Sudan Ya Kai 528
Kazamin rikicin da ake tafkawa tsakanin rundunar sojin Sudan da rundunar RSF, ya yi sanadin rayuka akalla 528 da raunata wasu 4,599.
Rahoton da ma’aikatar lafiya ta kasar ta fitar jiya, ya ce tsawaita tsagaita bude wuta ya sa yanayi ya!-->!-->!-->…
Hukumar Kidaya Ta Yi Bayanin Dalilan Dage Aikin Kidaya Ana Daf Da Fara Shi
Hukumar Kidaya ta Kasa, NPC, ta ce an dage kidayar yawan jama’a da gidaje ta shekarar 2023 saboda shirin mika mulki ga sabuwar gwamnati da kuma yanayin da kasa ta shiga bayan zabubbukan 2023.
Manajan Kidaya na Shekarar 2023 Kuma!-->!-->!-->…
Sojoji Sun Farmaki Ofishin KAEDCO Da Ke Kebbi, Sun Ci Zarafin Ma’aikata Saboda Rashin Wutar Lantarki
Sojoji dauke da makamai sun kai farmaki ofishin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna KAEDCO a jihar Kebbi tare da cin zarafin ma’aikatan da suka kasa samar musu da wutar lantarki a barikinsu.
Manajan kamfanin na jihar Kebbi,!-->!-->!-->…
Ya Tabbata Gwamnatin Buhari Ta Fasa Gudanar Da Aikin Kidaya A Lokacinta
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da dage aikin kidayar jama’a da gidaje na shekarar 2023 wanda aka shirya gudanarwa a kwanakin 3 zuwa 7 ga watan Mayun gobe, har sai lokacin da sabuwar gwamnati ta ga dacewar gudanar da aikin.
!-->!-->!-->…
An Dakatar Da Cire Tallafin Man Fetur A Najeriya
Majalissar Zartarwa ta Kasa, NEC, ta dakatar da shirin janye tallafin man fetur wanda a baya aka tsara cirewa a watan Yunin bana bayan karewar wa’adin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Da take yiwa manema labarai jawabi jim kadan bayan!-->!-->!-->…
Masu Rubuta JAMB Sun Je Jarabawa Da Wukake, Sun Yi Barazanar Maganin Shugabannin Jarabawar
Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB, ta ce masu rubuta JAMB sun yi amfani da wukake wajen yin barazana ga jami’an hukumar.
Zargin ya biyo bayan rahotannin da suka nuna cewa, JAMB ta tabbatar da cewa, masu rubuta!-->!-->!-->…
Hukumar Lafiya Ta Gargadi Mutane Kan Shan Wani Maganin Tari Na Indiya
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce an gano wasu tarin jabun magungunan tari da Indiya ta yi a tsibirin Marshall da ke Micronesia.
WHO ta ce gwajin maganin tarin mai suna Guaifenesin TG wanda kamfanin haɗa magunguna na QP Pharmachem!-->!-->!-->…
Tinubu Ya Rufe Kofa Da Wani Mai Neman Shugabancin Majalissar Wakilai
A jiya Talata ne mai neman shugabancin Majalissar Wakilai a majalissa ta 10, Dan Majalissa, Muktar Betara, ya rufe kofa da Shugaban Kasa Mai Jiran Gado, Bola Ahmed Tinubu.
Betara wanda shine Dan Majalissar Wakilai mai wakiltar mazabar!-->!-->!-->…
Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 6
A yau Laraba, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin manyan sakatarori shida kafin fara zaman Majalissar Zartarwa na yau.
A watan Maris da ya gabata ne, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin manyan sakatarorin.
!-->!-->!-->!-->!-->…
Ba A Samu Sanya Hannun Jari Ko Na Sisi Ba A Wasu Jihohi 8 Na Najeriya
Akalla jihohi takwas ne ba su iya jan hankalin masu sanya hannun jari daga kasashen waje ba amma bashin da suka ciyo ya kai naira biliyan 194.09 a tsakanin shekarar 2019 da 2022 kamar yanda jaridar PUNCH ta gano.
Bayanai daga Hukumar!-->!-->!-->…
A Watanni 12 Kacal, Najeriya Ta Yi Asarar Naira Tiriliyan 2.3 A Satar Danyen Mai
Najeriya ta yi asarar damar fitarwa da siyar da danyen mai kimanin ganga miliyan 65,700,000 a shekara daya da ta gabata saboda lalata bututun mai da yake jawo sace danyen man.
Wannan adadi na gangunan da aka sace, ya sanya Najeriya ta!-->!-->!-->…
An Baiwa ‘Yan Kasashen Waje 385 Damar Kasancewa ‘Yan Najeriya
A jiya Laraba ne Majalissar Zartarwa ta Kasa ta amince da bayar da damar kasancewa ‘yan Najeriya ga ‘yan kasashen waje mutum 385 da ke zaune a kasar.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya ce, mutane 317 cikin masu neman!-->!-->!-->…
Gwamnati Ta Dakatar Shugaban Hukumar Kula Ilimin Sakandire Saboda Zargin Cinhanci
An dakatar Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Sakandire ta Kasa, NSSEC, Farfesa Benjamin Abakpa saboda zargin badakalar kudade.
Dakatarwa ta bayyana ne a takardar da Babban Sakatare na Ma’aikatar Ilimi ta Kasa, Andrew David Adejo ya!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya, Jihohi Da Kananan Hukumomi Sun Raba Kudin Maris Naira Biliyan 714.629
Kwamitin Rarraba Kudaden Tarayya, FAAC, ya raba naira biliyan 714.629 ga rukunonin gwamnati uku na Najeriya jiya Laraba a Abuja a matsayin kudin watan Maris.
Wannan labari ya samu ne daga sanarwar bayan taro da aka saki a karshen zaman!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya Ta Bayar Da Hutun Karamar Sallah
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a 21 da Litinin 24 ga watan Afrilu, 2023 a matsayin ranakun hutun Karamar Sallah a Najeriya.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da hutun a madadin Gwamnatin Tarayyar, kamar!-->!-->!-->…
Zazzabin Lassa Ya Watsu Cikin Jihohi 26 Na Najeriya, Ya Kashe Mutane 151
Mutuwa a sanadiyyar zazzabin Lassa a Najeriya ta karu a bana zuwa 151 daga 148, kamar yanda Hukumar Kare Yaduwar Cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sanar.
A rahotonta na mako na 14, NCDC ta ce, an samu rahoton kamuwa da zazzabin Lassa 869!-->!-->!-->…
Buhari Ya Dawo Abuja Bayan Kwashe Kwanaki 8 A Saudiyya
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja bayan ziyarar kwanaki 8 a kasar Saudiyya, inda ya kuma gabatar da aikin Umara.
Shugaban na Najeriya ya bar Filin Jirgin King Abdulaziz da ke Jiddah a kasar Saudiyya a yau Laraba.
Kamfanin!-->!-->!-->!-->!-->…
Sabon Dan Majalissar Wakilai Ya Bayar Da Gudunmawar Shanu 59 Don Bikin Sallah A Mazabarsa
Sabon Dan Majalissar Wakilai mai jiran rantsuwa na Mazabar Gwamnatin Tarayya ta Maru/Bungudu a Jihar Zamfara, Abdulmalik Zubairu a jiya Talata, ya bayar da gudunmawar shanu 59 ga al’ummar mazabarsa domin gudanar da bikin karamar sallah.
!-->!-->!-->…
Binani Ta Musanta Zargin Cewa Ta Bayar Da Cinhancin Biliyan 2 Don Ta Ci Zabe
‘Yar takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan Jihar Adamawa da ya gabata, Sanata Aishatu Dahiru, wadda aka fi sani da Binani, ta musanta zarge-zargen da ake mata na cewa ta baiwa wasu jami’an Hukumar Zabe mai Zamanta Kanta ta Kasa, INEC, ciki!-->…
Fintiri Ya Lashe Zaben Gwamnan Adamawa
Hukumar zaɓe a Najeriya ta sanar da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar Adamawa, wanda ya ƙare cikin taƙaddama.
Jami'in sanar da sakamakon zaɓen gwamna na Adamawa, Farfesa Mohammed Mele ya ce Ahmadu Fintiri!-->!-->!-->…