Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
Security
Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 152, Sun Kama 109, Sun Ceto Mutane 91
Sojoji sun kashe ƴan ta’adda 152, sun kama 109, sun ceto mutane 91 da aka yi garkuwa da su, a yayin da suke yaƙi da matsalar tsaro a fadin kasar nan cikin makon da ya gabata.
Sojojin sun kai hari kan sansanonin wasu manyan shugabannin!-->!-->!-->…
Yanda Ƴanbindiga Suka Ciyar Da Karnukansu Naman Direban Ƴan’uwana – Wani Malami A Sokoto
Sheikh Bashar Danfili, wani sannanen malami a Jihar Sokoto, ya nemi taimakon kudi daga jama’a bayan ƴan bindiga sun sace ƴan’uwansa guda shida a hanyarsu zuwa wani ƙauye a jihar.
Ya bayyana hakan ne a cikin wani gajeren bidiyo da ya!-->!-->!-->…
Ƴanta’adda Sun Mayar Mu Bayi, Suna Sa Mu Aiki A Gonakinsu – Ƴan Jihar Niger
Mutanen da ke zaune a wasu garuruwa da ke fama da matsalar tsaro a Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja, sun koka cewa ƴan ta’adda da ƴan bindiga na bautar da su wajen aikin gona a gonakin su.
An gano cewar, shugaban wata ƙungiyar!-->!-->!-->…
Ƴanbindiga Sun Kama Mutum 22 A Wani Sabon Hari A Kaduna
A wasu hare-hare daban-daban da aka kai, ƴan bindiga sun sace mutum 19 a unguwar Mani kusa da wani kamfani a Mazaɓar Rido da ke Ƙaramar Hukumar Chikun da kuma yankin Danhonu II Millennium City a Kaduna.
A garin na Mani, ƴan bindigar sun!-->!-->!-->…
Fursunoni 3,590 Na Jiran Hukuncin Kisa A Najeriya – NCoS
Akalla fursunoni 3,590 ne da ke cikin gidajen gyaran hali a fadin Najeriya ke jiran hukuncin kisa, kamar yanda Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) ta bayyana.
Mai magana da yawun hukumar, Mataimakin ACC Abubakar Umar,!-->!-->!-->…
Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Kakkaɓe Ƴanbindiga Yayin Da Minista, CDS Suka Isa Sokoto
A jiya ne Gwamnatin Tarayya ta bakin Ƙaramin Ministan Tsaro, Dr. Bello Matawalle, ta sha alwashin kakkaɓe ƴanbindiga da sauran gungun masu aikata laifuka da ke addabar yankin arewa maso yamma, biyo bayan umarnin Shugaban Kasa Bola Tinubu!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Ƴan Sanda Sun Ayyana Baturen Birtaniya Da Ɗan Najeriya a Matsayin Wadanda Ake Nema…
Rundunar ‘Yansandan Najeriya, a ranar Litinin, ta bayyana wani ɗan ƙasar Birtaniya mai suna Andrew Wynne, wanda kuma aka sani da Andrew Povich, da wani dan Najeriya mai suna Lucky Obiyan, a matsayin wadanda ake nema saboda zargin yunkurin!-->…
Yanda Zanga-Zangar #EndBadGovernance Ta Sa Tinubu Ya Kori Shugabannin DSS Da NIA
Dalilan da suka sa tsohon Darakta-Janar na Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), Yusuf Bichi, da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA), Ahmed Abubakar, suka sauka daga mukamansu sun bayyana.
Wata majiya daga fadar shugaban ƙasa!-->!-->!-->…
An Yi Garkuwa Da Wasu Ƴan China 2 A Ogun
Wasu ƴan China su biyu masu suna Chen Wenguang da Liang Ding sun faɗa hannun masu garkuwa da mutane a yankin Kemta/Abule-Owu da ke kan titin Onigbedu a Jihar Ogun.
Jaridar PUNCH ta gano cewar, an yi garkuwa da mutanen ne a jiya Lahadi!-->!-->!-->…
Ɗaruruwan Ƴan Boko Haram Sun Tsere Daga Wani Gidan Yari
Ɗaruruwan ƴan ta’adda, ɓatagari da masu safarar ƙwayoyi ne aka rawaito sun tsere daga wani gidan yari a Jamhuriyar Nijar.
Gidan yarin da ke kusa da babban birnin ƙasar, Niamey, ya fuskanci mummunan hari a jiya Alhamis, inda aka rinjayi!-->!-->!-->…
Kotu Ta Saki Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah, Bodejo
Alƙali Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya ya kori ƙarar zargin ta’addanci da ake yi wa Bello Bodejo, Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore biyo bayan buƙatar Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya na a kori ƙarar.
A baya dai kotun ta!-->!-->!-->…
Wata Ƙungiyar Sarakunan Gargajiya Ta Yi Kira Ga Sarki Sunusi Da Ya Girmama Kotu, Ya Fice Daga Fadar…
Ƙungiyar Sarakunan Gargajiya a Najeriya ta shawarci Sarki Sunusi Lamido Sunusi da ya girmama umarnin Babbar Kotun Tarayya, ya sauƙa daga karagar mulkin Kano nan take.
Sarakunan sun ce, hukuncin kotun da ta bayar ranar Talata, hukunci ne!-->!-->!-->…
Ƴansanda Da Sojoji Sun Bijirewa Gwamnan Kano, Sun Ce Zasu Tabbatar Da Umurnin Kotu Na Dakatar Da…
Jami'an tsaro a Kano sun ce sun karbi umarnin kotu kuma za su yi amfani da shi tare da samar da cikakken tsaro a faɗin jihar Kano.
Cikin wani jawabin hadin gwiwa da jami'an tsaron suka gabatar wa manema labarai a shalkwatar 'yan sanda!-->!-->!-->…
Ƴanbindiga Sun Kashe Ƴansanda Biyu A Enugu
A jiya Juma’a da daddare ne wasu ƴanbindiga suka kashe ƴansanda biyu da ke Rundunar Ƴansanda ta Jihar Enugu.
Ƴansandan da ke aiki ƙarƙashin Ofishin Yankin Ogui an ce suna kan aikinsu ne na binciken ababen hawa a kan titin Presidential!-->!-->!-->…
Shugaban Miyatti Allah Ya Ce Ba Shi Da Wata Alaƙa Da Ta’addanci
Shugaban Miyatti Allah Kautal Hore, Alhaji Bello Bodejo, wanda ke fuskantar tuhume-tuhumen ta’addanci ya buƙaci kotu da ta bayar da belinsa, inda ya ce ba shi da wani tarihi na aikata ta’addanci.
Bodejo wanda ke fuskantar tuhuma a!-->!-->!-->…
Ƴansanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane A Kaduna
Rundunar Ƴansanda Reshen Jihar Kaduna ta kama wani mai suna Bello Muhammad mai shekaru 28 ɗan asalin Jihar Zamfara da ake zargi da yin garkuwa da mutane tare da ƙwato naira miliyan 2 da ake zargin ya karɓa ne daga iyalan waɗanda yake!-->…
Soja Na Samun Ƙasa Da Naira 50,000 A Wata – In Ji Babban Hafsan Sojojin Najeriya
Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Janaral Christopher Musa ya bayyana cewar ana biyan sojojin Najeriya albashin naira 50,000 ne a kowanne wata, yayin da shi kansa da sauran sojoji ke samun naira 1,200 a matsayin alawuns na aiki a kowacce!-->…
Gwamonin Arewa 19 Sun Ziyarci Kaduna, Sun Bayar Da Gudunmawar Kuɗi Ga Mutanen Tudun Biri
Gwamonin Arewa 19 sun haɗu jiya Juma’a a Kaduna domin tattaunawa kan yanda za a magance matsalar tsaro, bunƙasa noma, haƙo mai a yankin Arewa da kuma jajantawa Gwamnan Kaduna Uba Sani kan iftila’in da ya jawo asarar rayuka da dama a Tudun!-->…
Ana Zargin Wani Basarake Da Yin Fyaɗe Da Sa Wa Yarinya Ƙanjamau A Jigawa
Ana zargin Digacin Ɗan Gulam da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram a Jihar Jigawa, Umar Ibrahim da yin fyaɗe da yi wa yarinya mai suna Hannatu Yahaya ciki da kuma sanya mata cutar ƙanjamau.
Wannan na ƙunshe ne a wasiƙar da Babban Mai Shigar da!-->!-->!-->…
Hanyar Sadarwar Al’ummar Gaza Ta Katse Yayin Da Isra’ila Ta Tsananta Luguden Wuta
A daren da ya gabata Isra'ila ta tsananta luguden wuta kan yankin Gaza fiye da sauran darare a baya, lamarin da ya sanya aka gaza sadarwa da al'ummar yankin, abin da ke nuna cewa da alama hanyoyin sadarwa sun katse.
Isra'ila a ɓangare!-->!-->!-->…