Sign in
Sign in
Recover your password.
A password will be e-mailed to you.
Browsing Category
War and Conflict
Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Birnin Yenagoa Na Jihar Bayelsa
Mamakon ruwan sama da aka yi daga ranar Talata zuwa Laraba ya jawo ambaliyar ruwa a yankuna da dama na Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa.
Yankunan da suka fi shan wahala sun haɗa da maƙabarta, Azikoro, Ekeki, Okaka, Swali, Kpansia,!-->!-->!-->…
Mutane Rabin Miliyan Ne Suka Rasa Gidajensu Yayin Da Mutane 30 Suka Mutu A Ambaliyar Ruwan Borno
Aƙalla mutane 414,000 ne suka rasa matsugunansu yayin da wasu 30 suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, a ranar Talatar da ta gabata.
Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa!-->!-->!-->…
NiMet Ta Ce A Gujewa Yankunan Da Ke Da Haɗarin Ambaliya, Yayin Da Ake Sa Ran Samun Ruwan Sama Mai…
Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama mai ƙarfi da iska daga ranar Laraba zuwa Juma’a a sassan kasar nan.
A cikin rahoton yanayi da ta fitar a jiya Talata, NiMet ta ce ana sa ran za a sami!-->!-->!-->…
AMBALIYAR RUWA: Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Sansanonin Ƴan Gudun Hijira Yayin Da Ambaliya Ta Mamaye…
Dubban mutane sun rasa matsugunansu a Maiduguri yayin da Hukumar Kula da Gidajen Gyara Hali ta Najeriya ta sake kamo fursunoni uku da suka tsere bayan rugujewar kurkuku, sannan kashi 80% na dabbobin gidan zoo na Sanda Kyarimi sun mutu!-->…
AMBALIYAR RUWA: Macizai, Kadoji Da Sauran Muggan Dabbobi Sum Mamaye Borno
Wata sanarwa daga Gidan Adana Kayan Tarihi na Jihar Borno ta bayyana cewa dabbobin daji masu haɗari sun kutsa cikin unguwannin Maiduguri saboda ambaliyar ruwan da ta mamaye birnin.
Babban Manajan gidan, Ali Abatcha Don Best ne ya!-->!-->!-->…
Ambaliyar Ruwa Ta Cinye Fadar Shehun Borno, Ta Raba Mutane Da Gidajensu
Ambaliyar ruwa ta mamaye fadar Shehun Borno, Alhaji Garbai Elkanemi, da wasu sassan birnin Maiduguri a farkon safiyar yau Talata, inda hakan ya tilastawa mutane barin gidajensu.
Wani rahoto ya bayyana cewa Shehun Borno ya bar fadarsa!-->!-->!-->…
YANZUNNAN: Mutum 2 Sun Mutu, 2 Sun Jikkata A Rugujewar Gini A Kano
Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane biyu da jikkatar wasu biyu a lokacin da wani bene mai hawa biyu ya rufta a unguwar Noman’s Land, da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a Jihar Kano.
Dr. Nuraddeen!-->!-->!-->…
Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Jihohi 29 Na Najeriya
Ambaliyar ruwa mai tsanani ta shafi jihohi 29 na ƙasar nan, inda adadin mutanen da suka mutu ya ƙaru zuwa 192, a cewar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA).
Ambaliyar, wadda aka alaƙanta da samun yawaitar ruwan sama da kuma!-->!-->!-->…
Wasu Ƴanmata 3 Sun Mutu A Jigawa Sanadiyyar Nutsewa A Cikin Ruwa
Wasu ƴanmata guda uku sun mutu a sanadiyyar nutsewa a ruwa da misalin ƙarfe 11 na ranar Asabar a wani gulbi da ke yankin Ƙaramar Hukumar Buji a Jihar Jigawa.
Ƴanmata sun faɗa wannan hatsarin ne lokacin da suke yin ciyawa domin kaiwa!-->!-->!-->…
YANZU-YANZU: Mutane Da Dama Sun Mutu Yayin Da Wasu Su Ka Maƙale A Dogon Benin Da Ya Rushe A Abuja
Wani beni mai hawa da dama da ke kan Lagos Street a yankin Garki da ke Abuja ya rushe, inda mutane kusan 37 suka rasa rayukansu wasu kuma da dama suka maƙale a cikin ɓaraguzai, in ji PUNCH.
Lamarin dai ya faru ne a daren jiya Laraba!-->!-->!-->…
YANZU-YANZU: Jirgin Sojan Saman Najeriya Ya Yi Hatsari A Jihar Neja
Wani jirgin saman sojoji mallakin Rundunar Sojan Saman Najeriya, NAF, ya yi hatsari.
Jirgin dai ya tashi ne daga Kaduna yana kan hanyarsa ta zuwa Minna, babban birnin Jihar Neja lokacin da hatsarin ya faru.
Da yake tabbatar da!-->!-->!-->!-->!-->…
Masallata 8 Ne Suka Rasu, 25 Suka Sami Raunuka A Dalilin Rushewar Babban Masallacin Zaria
A ƙalla masallata takwas ne suka rasu, yayinda 25 suka ssamu raunuka a dalilin rugujewar wani sashi na Babban Masallacin Zaria mai shekaru 150 da ginawa.
Wannan ibtila’i dai ya faru ne a jiya Juma’a lokacin sallar La’asar a garin na!-->!-->!-->…
Mamakon Ruwan Sama Ya Kashe Mutane 33 Tare Da Ɓatar Da 18 A Beijing
Wani mamakon ruwan saman da ba a taɓa ganin irinsa ba a Beijing ta Ƙasar China a yau Laraba, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 33 da kuma ɓatar da wasu su 18, in ji jami’an gwamnatin ƙasar.
Jami’an sun ƙara da cewar, mamakon ruwan saman!-->!-->!-->…
Yiyuwar Ambaliyar Ruwa A Hadejia: Shin Mene Ne Shirin Karamar Hukuma?
Daga: Ahmed Ilallah
A bana ma Jihar Jigawa na daga cikin jihojin da za su fuskanci ambaliyar ruwa. Gashi kuma har yanzu mutanen da suka fuskanci ibtila'in ambaliyar bara, basu fita daga yanayin da suka samu kan su ba.
Karamar Hukumar!-->!-->!-->!-->!-->…
Mutane 3 Sun Mutu, 13 Sun Jikkata A Yayinda Bus Ta Kama Da Wuta A Kano
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce, fasinjoji mata uku ne suka rasa rayukansu yayinda fasinjoji 13 suka sami raunuka lokacin da wata motar bus ta haya ta kama da wuta a jiya Talata.
Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Alhaji!-->!-->!-->…
Mummunar Tsawa Ta Kashe Mutum 10 A Mozambique – Majalissar Dinkin Duniya
Majalisar Dinkin Duniya ta ce tsawa ta hallaka mutuane 10 bayan mamakon ruwan sama da kuma afkuwar wata mahaukaciyar guguwa a Mozambique.
Ofishin bayar da agaji na Majalissar Dinkin Duniya ta ƙara bayar da sanar cewa wasu mutum 11 sun!-->!-->!-->…
Gobara Ta Lakume Dukiya Mai Yawa A Kauyukan Jigawa
Gobara ta lalata dukiya ta miliyoyin kudi a kauyukan Malamawar Dangoli, Karangi da Kwalele da Karamar Hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa.
Gobarar da ta faru a ranar Lahadi, ta lalata gidaje tare da kona dabbobi, kayan gona da sauran!-->!-->!-->…
Garin Saka Caji, Lantarki Ta Ja Wata Mata ‘Yar 36 Har Lahira A Taraba
Wata mata ‘yar shekara 36 ta mutu a dalilin jan da wutar lantarki tai mata a garin Jalingo na Jihar Taraba.
Matar, wadda aka bayyana sunanta da Jindori Ignatius ‘yar kabilar Kona, ta mutu ne a lokacin da kake kokarin sanya cajin wayarta!-->!-->!-->…
Hatsarin Mota Ya Kashe Mutane 6 A Bauchii – FRSC
Hukumar kiyaye afkuwar hatsura ta ce mutane shida ne suka mutu yayin da biyu suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya afku a ƙauyen Dinki da ke jihar Bauchi.
BBC Hausa ta rawaito cewa, hukumar ta ce hatsarin motar ya faru ne bayan!-->!-->!-->…
Wutar Lantarki Ta Kashe Mutane 11, Ta Kuma Jiwa Wasu Da Dama Raunuka A Zaria
A kalla mutane 11 ne wutar lantarki ta kashe har lahira, yayin da wasu da dama suka samu raunuka a Karamar Hukumar Zaria da ke Jihar Kaduna.
Hatsarin ya faru ne a ranar Laraba da rana a yankin Gwargwaje na karamar hukumar, inda ya jawo!-->!-->!-->…