A jiya Juma’a an ta yada fastocin yakin neman zaben Peter Obi manne a jikin tabarmin sallar Musulmi, abin da ya jawo cecekuce musamman a kafafen sa da zumunta.
An ta yada hotunan abin da ya jawo kushe ga Musulmai wadanda addininsu ya hana manna hotuna a jikin kayan da ake amfani da su yayin ibada.
Duk da cewa Peter Obi ya barranta kansa da fastocin, mutane da dama sun yi allawadai da lamarin.
Wasu gungun magoya bayan Obi ne suka yi fastocin a jikin tabarmin domin su baiwa masu zabe Musulmi a matsayin tukuici.
Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, kuma dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya bayyana a shafinsa na Twitter cewar, tabarmin ba daga ofishin yakin neman zabensa suke ba.
Ya kuma ce, “Sanya hotona a jikin tabarmin salla abu ne da bai kamata ba, duk da an yi hakan da kyakkyawar niyya, amma hakan bai fito daga ofishin yakin neman zabe na ba. Ina matukar girmama addinin Musulunci da ma sauran addinai. Ba zamu taba wulakanta wani addini, kabila ko jinsi ba. Mu ‘yan Najeriya ne guda daya.”