Daga: Ahmed Ilallah
Koda yake a tarihance gwamnatin Buhari ita tafi kowace gwamnati imanin cin bashi don cike gibin kasafin kudi, wanda a yanzu a na bin kasar nan zunzurutun bashin da ya haura N40trl. Koda a kasafin kudin bana ma na kimanin N22trl sai an cike gibin sama da N11trl ta hanyar bashi da sai da kadarorin gwamnati.
Ganin yadda a ka shiga takon saka tsakanin Majalissar Dokoki da kuma ta zartarwa a kan maganar bashi, ya sanya gwamnatin Buhari karkata wajen sayar da kadarorin gwamnati. Wanda yanzu gwamnatin ke aniyar sayar da kamfanonin wutar lantarkin ta a cikin farkon watanni ukun wannan shekarar, don kawai a samu kudin biyan kwangiloli.
Amma fa abin lura ma anan shine, wai mai ya sa wannan gwamnatin baza tana dinka riga iya wuyan ta ba?
A game da chefanar da kamfanonin gwamnati, wata nasara a ka taba cinmawa.
A misali, kamfanin sadarwa na NITEL wanda yake mallakar gwamnatin tarayyane. An kiyasta darajar sa a 2001 a kan $4bl, yayin da a ka sayar da kashi 51 a $2bl, amma daga baya cinikin ya gagara, a ka sake sayarwa $500ml, kai a karshe wannan kamfanin tarwatsa shi a kayi.
In mun dawo kan batun chefanar kanfunan WUTAR LANTARKI kuwa, in muka tuna baya, a irin wannan lokacin ne, gwamnatin baya ta chefanar da kamfanonin da suke rarraba wutar lantarki, wanda ya jawo kace na cane, domin wayanda a ka sayarwa wutar nan, basu da kwarewar inganta taba wutar, basu karfin jarin sanya wa don bunkasa kamfanonin, har gazawar su ta kai sun kasa cimma burin yan Nijeriya a kan al’amuran wutar lantarki.
Saboda gazawar su ma, kudaden da wasu daga kamfanoni suka ara a bankuna don sayan kamfanonin ma, sun gagara biyan bankuna bashin su, har ta kai a yanzu wasu bankunan sun kwace wannan kamfanoni a hannun su.
Duka wannan gazawa ce ta hukumomin sayar da kadarorin gwamnati wato NCP da BPE, domin sau tari babu wata nasara da a ke samu a akasarin kamfanonin da a ka sayar wa na gwamnati.
Ko a yanzu ba karamin ganganci ba Gwamnatin Buhari zata yi ba, in har ta dage a kan sai ta chefanar da kamfanonin wutar lantarkin kasar nan a wannan kuraren lokacin.
Na farko a kasa da wata uku, zaiyi mutukar wahala samu damn tantancewar kwararrun kamfanonin da ya kamata a sayar wa.
Na buyi a kwai rashin nasarar a wajen BPE na sai da kadarorin gwamnati ga wanda ya dace, sannan sayarwa ta dace da manufar tattalin Nijeriya.
Uwa uba, bunkasar cin hanci da rashawa a wannan kasa da shigar da san rai wajen chefanar da kadarorin gwamnati, zai sanya wannan gwamnatin ma zata tafka babban kuskure, wanda hakan ya nuna karara, Gwamnatin Buhari ta gaza banbance kanta da takwarorin ta na baya.
alhajilallah@gmail.com