For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Charles Soludo Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Anambara

Daga: Kabiru Zubairu

Farfesa Charlse Soludo na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra, inda ya cinye kananan hukumomi 19 cikin 21 na jihar.

“Charles Chukwuma Soludo na jam’iyyar APGA, ganin cewa ya cika dukkan ka’idoji na doka, hakan ya sa ya zama wanda yai nasara a zabe kuma ya zama zababbe,” in ji Mai Sanar da Sakamakon Zabe daga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, Farfesa Florence Obi, yayin da yake fadin sakamakon zaben gwamnan Anambra a yau Laraba da safe.

‘Yan takarkarun jam’iyyun Peoples Democratic Party, PDP, Mr Valentine Ozigbo, da na jam’iyyar Young Progressives Party, YPP, Senator Ifeanyi Ubah, dukkanninsu sun ci kananan hukumomi dai-dai.

Sai dai dantakarar jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Senator Andy Uba bai samu nasarar cin ko karamar hukuma daya ba.

Soludo wanda, dan shekaru 61 ne, kuma tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, ya sami kuri’u 112,229 ninki biyun abin da mabiyinsa daga jam’iyyar PDP, Ozigbo ya samu, wanda hakan ya sa Soludo ya lashe zaben.

Ozigbo ya samu kuri’u 53,807 sai sauran biyun da suka biyo bayansa, Uba da Ubah suka sami kuri’u 43,285 da 21,261.

Adadin masu rijistar zabe a jihar ta Anambra shine 2,466,638, yayin da aka tantance masu yin zabe 253,388 domin yin zaben gwamnan.

An kada lafiyayyun kuri’u guda 241,523, yayin da aka sami kuri’u 8,108 lalatattu, wanda ya nuna cewa an kada kuri’u 249,631 gaba daya a zaben gwamnan.

Comments
Loading...