Kasar China ta doke Najeriya da ci 90 da 76 a wasan da suka buga na share fagen shiga gasar kwallon kwando ta mata ta duniya FIBA, a wasansu na rukunin B da suka buga a birnin Belgrade na kasar Serbia a ranar Alhamis.
Kociyan wasan kasar Chaina Zheng Wei, ta bayyana hakan bayan buga wasan, ta ce ’yan wasanta sun taka rawar gani ta fuskar kai hari da kuma tsare gida a zagayen farko na wasan, kuma sun shirya wa wasan yadda ya kamata, amma ba su yi wasa mai kyau ba a zagaye na biyu.
Kociyan Najeriya Otis Hughley Jr. ya ce, hakika ’yan wasan kasar China sun bada mamaki, babu wani batun bada uzuri, sai dai ya bayyana kyakkyawan fatan samun nasarar tawagar ’yan wasansa a wasansu na gaba.
Yar wasan Najeriya Amy Okonkwo ta ce, Najeriya ta fito da su kuma ta yi musu dukkan abin da ya dace, don haka za su koyi darasi daga kuskurensu domin lashe ragowar wasanninsu biyu don samun nasarar tsallakawa gasar kofin duniya.
A gobe kasar China za ta buga wasanta na gaba inda za ta kara da Mali, yayin da Najeriya za ta fafata da Faransa.