For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Cikin Shekaru 7 APC Ta Yi Abin Kirkin Da Ya Fi Na PDP – Shugaban APC

Shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya baiyana cewa, jam’iyyar APC mai mulki, cikin shekaru 7, ta cimma nasarorin da babu wata jam’iyya a ƙasar nan da ta iya cimmawa.

Abdullahi Adamu, ya baiyana hakan ne a jiya Talata, a wajen ƙaddamar da fara tantance masu neman yiwa jam’iyyar APC takarar majalissun jihohi a zaɓen shekarar 2023 mai zuwa.

Shugaban jam’iyyar, wanda Mataimakin Shugaban Jam’iyya (na yankin Arewa), Sanata Abubakar Kyari ya wakilta, ya baiyana cewa ba ya tantamar cewa, dukkanin masu neman takarar da za a tantance za su ɗora da abubuwan alkhairin da jam’iyyar ke gabatarwa.

Ya ce, za su iya bugar ƙirji bayan samun nasarori a shekaru 7 wadanda wasu suka kasa samu a lokacinsu.

Ya ƙara da cewa, sauyin mulkin da za’a samu a shekarar 2023 shine abun alkhairi na ƙarshe da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai bari ga ƴan Najeriya.

Rahotannin da TaskarYanci ta samu, sun nuna cewar akwai aƙalla ƴan-takarkaru 3000 da ke neman hayewa kujerun majalissun jihohi a APC.

Wadannan ƴan-takarkaru, sun sayi fom ɗin tsayawa takarar ne a kan Naira Miliyan Biyu kowannesu kafin ƙarewar wa’adin siyarwar a makon da ya gabata.

Comments
Loading...