For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Cikin Watanni 11, Najeriya Ta Tura Sojoji 640 Su Temakawa Ƙasashen Waje Alhali Ƙasar Na Cikin Matsalar Tsaro

Najeriya ta tura sojojin da ba su gaza 640 ba zuwa samar da zaman lafiya daban-daban a ƙasashen wajen ana tsaka da matsalar tsaro a faɗin ƙasar.

An samo adadin sojojin ne daga rahotannin kafafen yaɗa labarai waɗanda aka duba tsakanin watan Yuli na shekarar 2021 zuwa watan Mayu na shekarar nan da muke ciki.

A ranar 21 ga watan Yuli na shekarar 2021 ne, Ministan Tsaro, Major General Bashir Magashi ya ce, sama da sojojin Najeriya 200 ne ke aiki a shirin samar da zaman lafiya na Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, wanda ake gudanarwa a Gambia.

Sannan kuma a ranar 3 ga watan Disamba na shekarar 2021, an tura sojoji 62 zuwa Mali domin shirin samar da zaman lafiya, haka kuma, a ranar 21 ga watan Afrilu na shekarar nan da muke ciki ne, aka tura sojojin da ba su gaza 173 ba zuwa shirin samar da zaman lafiya a ƙasar Guinea Bissau.

Haka dai, a ranar 30 ga watan na Afrilu Rundunar Sojojin Najeriya ta tura sojojin ko ta kwana guda 205 zuwa ƙasar Gambia domin shirin samar da zaman lafiya.

A rahoton da SBM Intelligence ta saki, an kashe aƙalla mutane 2,085 a Najeriya, tsakanin watan Oktoba zuwa Disamba na shekarar 2021, a tashin hankali daban-daban da suka faru a faɗin ƙasar, yayin da aka haɗa jimillar waɗanda suka rasa rayukansu a shekarar ta 2021 da cewa, sun kai 10,366.

Haka kuma, a tsakanin watan Janairu da watan Maris na shekarar 2022 da muke ciki, aƙalla mutane 2,968 aka kashe, yayin da aka yi garkuwa da mutane 1,484 kamar dai yanda bayanai suka nuna daga Nigeria Security Tracker.

Su kansu jami’an tsaron ba su tsira ba, inda aka kashe jami’an tsaro aƙalla 323 a tsakanin watan Janairu zuwa 15 ga watan Mayu na shekarar 2022.

Masana harkokin tsaro da dama da jaridar PUNCH ta tuntuɓa sun kushe matakin Gwamnatin Tarayya na tura sojoji ƙasashen waje, alhali ƙasar na fama da matsananciyar matsalar tsaro.

Comments
Loading...