Kusan masana’antu 100 ne aka rufe a Kano saboda katsewar wutar lantarki a cikin watanni uku.
Kano dai ita ce cibiyar kasuwanci ta yankin arewacin Najeriya tun kafin ‘yancin kai har kawo yanzu.
A wata tattaunawa da Shugaban Kungiyar Masu Masana’antu ta Najeriya, reshen Jihar Kano da Jigawa, Alhaji Sani Husseini ya bayyana cewa, kusan masana’antu 100 ne suka rufe a cikin watanni uku saboda katsewar wutar lantarki da kuma hauhawar farashin man dizel.
A bangaren rasa aiyuka kuma Sani ya bayyanawa wakilin NIGERIAN TRACKER cewa, kusan ma’aikata 2000 ne suka rasa aiki saboda rufe masana’antun.
Ya kuma ce, iya masana’antun da ke sarrafa muhimman kayan amfanin yau da kullum ne suka iya jure yanayin, yayin da su ma wasu suka rage aikinsu zuwa rabin yanda suke yi a da.
Ya kara da cewa, dole ce ta sa wadanda suka rufe masana’antun suka rufe, domin ko da sun yi kokari sun sarrafa kayayyakin da suke sarrafawa al’umma ba sa iya siya saboda tsada da kuma talauci da ake fama da shi.
Alhaji Sani Husseini ya yi kira ga gwamnati da ta dau matakan rage tsadar man dizel ko masana’antu a Arewa sa rayu kamar takwarorinsu na yankin Kudu.