Shugaban Shirya Babban Taron Jam’iyyar Peoples Democratic Party na 2022, Sanata David Mark, ya baiyana karuwar matsalar tsaro, rashin aikin yi, cin hanci da rashawa da talauci a kasa a matsayin alamar mulkin jam’iyyar All Progressives Congress, APC wadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke jagoranta.
Ya baiyana cewa, gwamnati mai ci ta sanya rayuwa a Najeriya ta zama mai tsananin wahala.
David Mark ya baiyana hakan ne a cikin jawabinsa na maraba a lokacin taron zaben fidda gwani na PDP a Abuja a yau Asabar.
Ya ce, “’Yanuwanmu ‘yan kasa maza da mata a yau suna kame a wajen masu garkuwa da mutane, kuma gwamnatinmu tana gani ta kasa cetonsu. Abin haushi, gwamnatin APC ta cefanar da goben ‘yan Najeriya ta hanyar ciyo bashi ba tare da abin alheri ba. Najeriya a yanzu haka ita ce, cibiyar talauci ta duniya.
Ya kara da cewa, a yanzu haka alamar gane mulkin jam’iyyar APC sune karuwar rashin aikin yi, talauci, rashin dacewa, cin hanci da rashawa, uwa uba ma rashin iya magance rarrabe-rarrabenmu.
Davida Mark ya kuma soki gwamnatin kan yajin aikin Kungiyar ASUU da ya ki ci ya ki cinye wa, inda ya ce rashin iya magance yajin aikin ya samo asali ne daga gazawar gwamnatin wajen magfance matsalolin da suke addabar bangaren ilimi a Najeriya.