Najeriya ta samu karin koma baya da mataki biyar a kididdigar Kokarin Kasashe na Magance Matsalar Cin Hanci da Rashawa a Bangaren Gwamnati (Corruption Perceptions Index (CPI), ta shekarar 2021 wadda Kungiyar Tabbatar da Gaskiya da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Duniya (Transparency International (TI) ta saki ranar Talatar nan.
CPI ta gwada Najeriya, inda Najeriyar ta samu maki 24 cikin 100 na kokari a kididdigar shekarar 2021.
Wannan kididdiga ta sanya Najeriya a matsayin kasa ta 2 a Afirka ta Yamma wadda cin hanci da rashawa yaiwa kamari baya da kasar Guinea.
Wannan kididdiga ta sabawa kokarin da gwamnati take ikirarin yi na magance matsalar cin hanci da rashawa a Najeriya.
Matsayin Najeriya na yanzu, wato mataki na 154 cikin kasashe 180, koma baya ne kan matakinta na kididdigar shekarar 2020 wanda ta kasance ta 149 cikin kasashe 180.
Wannan kididdiga ta nuna cewa, cin hanci da rashawa a bangaren gwamnati karuwa yake ba raguwa ba.
Najeriyar ta samu maki 24 cikin 100 dari a shekarar ta 2021 wanda ya kasance koma baya ne da maki 1 kan makin da ta samu a 2020, kamar yanda TI bangaren Najeriya ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Talata.
Wannan shekara ta biyu kenan a jere da Najeriya ke samun koma baya a yaki da cin hanci da rashawa a kididdigar CPI.
Makin da kasar take samu yana samun koma baya daga shekarar 2019 inda ta samu maki 26 zuwa shekarar 2020 inda ta samu maki 25 da kuma na shekarar 2021 wanda ta samu maki 24.
Wannan kididdiga ta CPI da TI take gudanarwa ta nuna cewa, cikin shekaru 10 (daga shekarar 2012) Najeriya na cikin kasashe 27 wadanda cin hanci da rashawa yaiwa kamari a duniya.
A cikin jerin wadannan kasashe akwai Australia, Belgium, Botswana, Canada, Comoros, Cyprus, Dominica, Eswatini, Honduras, Hungary, Israel, Lebanon, Lesotho, Mongolia, Netherlands, Nicaragua, Niger, Nigeria, Philippines, Poland, Serbia, Slovenia, South Sudan, Switzerland, Thailand, Turkey da kuma Venezuela.