Shugaban Amurka Joe Biden, ya bayyana cinikin bayi a matsayin laifin asali na Amurka.
A cewar shugaba Joe Biden, sama da shekaru 400 da suka gabata, an tilasta kai wasu bayi 20 daga nahiyar Afrika zuwa gabar ruwan da yanzu ta samo Amurka. Daga bisani an sace tare da sayar da miliyoyi, cikin daruruwan shekarun da suka biyo baya, wani bangare na tsarin cinikin bayi dake zaman asalin laifin Amurka.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Fadar White House ta fitar jiya, a yunkurinta na tunawa da ranar 20 ga watan Augusta da aka ware a matsayin ranar tunawa da cinikin bayi a Amurka.
Sai dai ana ci gaba da ganin mummunan tasirin wannan tarihi har yanzu a Amurka, ciki har da kyama da wariyar launin fata, wanda har yanzu ke da tsanani a kasar.
(CRI Hausa)