Tsohon Shugaban Mulkin Soja, Abdussalami Abubakar ya yi magana kan yunkurin cire tallafin mai.
General Abdussalami, wanda yake jawabi a ranar Alhamis a wajen Taron Jin Ra’ayin Jama’a na Daily Trust a Abuja, ya bayyana cewa, Nigeria na fuskantar matsaloli da dama, wadanda cire tallafin mai zai kara ta’azzarawa.
Gwamnatin Tarayya dai ta ce, ta shirya dena biyan tallafin mai a watan Yuni, sai dai kuma shirin na fuskantar kalubalanta daga masu ruwa da tsaki da dama, ciki har da Kungiyar Kwadago.
Abdussalami ya ce, “Rashin aikin yi yana nan. . . kuma sama da ‘yan Nigeria miliyan 80 ne ke cikin matsanancin talauci.
“Duk wadannan suna cikin abubuwan da suke tasiri kan matsalar tsaro.
“Tabbas, Nigeria na fuskantar matsalar abinci wanda ke da alaka annobar COVID 19 da kuma rashin zaman lafiyar da ya addabi jihohi da dama na yankin Arewa.
“Duk wadannan sun jawo matsaloli da dama a duk fadin kasa, kuma sun tokare kokarin ‘yan Nigeria wajen samarwa da kuma yada abinci.
“Abin da ke faruwa shine cigaban hauhawar farashin abinci, wanda ya fi karfin gidaje da dama a Nigeria.
“Dadin dadawa, farashin mai na shirin kara tashi a watanni masu zuwa kamar yanda NNPC ta sanar a watan Nuwamban da ya gabata.
“Duk mun san cewa idan irin wannan ya faru, kamar yanda gwamnati ta tsara, zai kara jefa miliyoyi cikin matsanancin talauci.”