Daga: Kabiru Zubairu
Kungiyar CISLAC ta rubutawa Shugaban Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS korafi kan mamayen da wasu jami’ai sukaiwa ofishinsu a ranar Litinin da ta gabata.
A ranar Litinin din da ta gabata ne, wasu jami’an DSS suka yiwa ofishin Kungiyar Wayar da Kai kan Ayyukan ‘Yan Majalissu, CISLAC kawanya.
Ofishin CISLAC shine kuma cibiyar Najeriya ta kungiyar nan ta Transparency International, kungiyar da ke da rajin tabbatar da gaskiya a tafikar da gwanmnatoci, wanda ke yankin Jabi a Abuja.
Ranar Litinin din dai ta kasance daya daga cikin ranaku biyu na hutun Kirsimetin wannan shekara.
Babban Daraktan CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani ya bayyana cewa ba su sami wata sanarwa ko gayyata ba daga bangaren DSS kan zuwan jami’an.
Rafsanjani ya ce a lokacin sun yi zargin ko jami’an bogi ne ba na DSS ba, amma da suka kira daya daga cikin jami’an ya tabbatar musu da cewa shi jami’in DSS ne inda ya bayyana matsayinsa a hukumar.
Rafsanjani ya yi kira ga Shugaban DSS da ya gaggauta bincikar wadanda sukai wannan mamaye tare da jin hujjarsu ta yin hakan, musamman duba da yanda a yanzu ‘yan bindiga suke amfani da shigar jami’ai suna aikata laifuffuka.
Ya kuma yi kira ga shugaban da ya ladabtar da jami’an da kuma yin duk mai yiwuwa wajen kare mutuncin demokaradiyyar Najeriya.
A wasikar ta Rafsanjani, ya tabbatar da cewa CISLAC kungiya ce da ke kan doron doka, kuma tana biyayya ga tsare-tsaren doka ba tare da sun karya doka ba.