For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

CIWON SIKILA: Wata Kungiya Ta Ba Da Shawarar Yin Gwajin Jini Kafin Aure

Wata kungiya mai suna, Young Muslims Association of Nigeria (YMAN), ta ba da shawarar yin gwajin jini kafin aure ga ma’aurata.

Kungiyar ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi a karshen babban taronta na shekara-shekara karo na 38 da aka yi a Iworoko, wani yanki a Ado-Ekiti.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Malam Ismail Bello, Jami’in Hulda da Jama’a na kungiyar, ta ce yin gwajin ya zama dole domin dakile yawaitar cututtukan sikila a cikin al’umma.

Taron ya samu halartar wakilai sama da 480 daga kananan hukumomi 16 na jihar.

Bello ya ce ana bukatar irin wannan sa hannun don kare samuwar sabbin masu kamuwa da cutar sikila cikin sauki.

Bello ya ce kungiyar ta kuma bukaci Musulmai wadanda dukiyoyinsu suka kai zakka da su bayar da ita ta yanda za su amfanar da marasa galihu.

“Zakka tana daya daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar kuma umarni ne na Allah wanda kowane musulmi mai kishin addini dole ne ya kiyaye,” in ji shi.

Hakazalika, Bello ya umarci musulmai da su samar wa kansu isasshen ilimin Alƙur’ani Mai Tsarki a matsayin jagora don samun ceton har abada da ake fata.

Yayin da yake nuna rashin jin dadinsa da yanayin talauci a kasar, ya bukaci musulmai da su kasance masu kula da ‘yan uwansu ta hanyar sadaka.

“An gano talauci a matsayin daya daga cikin manyan matsalolin kasar.

“Idan an kawar da talauci, yawancin sauran matsalolin za su ragu sosai.

“Ingancin zakka a matsayin hanyar kawar da talauci ba abu ne da za a iya musawa ba.”

Bello ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da ta nemo mafita ta dindindin kan rashin tsaro, musamman, ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane domin ciyar da kasar gaba.

Sai dai, ya yabawa gwamnati kan yadda ta ke fadada anfani da irin tsare-tsaren kudade na Musulunci don bunkasa tattalin arziki.

Bello ya ce kungiyar ta kuma nemi yin taka tsantsan daga bangaren masu aikin yada labarai na kasar kan rahotoninsu bangaren ayyukan addini da abubuwan da suka faru don kada su kawo rikici.

“Batun da ke da nasaba da sanya hijabi da mata Musulmi ke bukata ya kamata a gaggauta magance shi ta hanyar tanadin tsarin mulki.

Ya kara da cewa “Babu wani hali da yakamata a ci zarafin wani dan Najeriya ko a hana shi hakkinsa saboda kiyayewa da bayyanar da imanin sa.”

Wasu daga cikin batutuwan da aka tattauna yayin taron sun haɗa da: Tsarin Addinin Musulunci a Dangantaka da Sauran Mabiya Addinai; Zaman Lafiya Tsakanin Al’umma: Hanyar Musulunci; da Zakka a Matsayin Mataki Mai Kyau don Kare Talauci.

Sauran su ne: Nauyin Ciwon Sickle Cell; Muhimmancin Binciken Kwayoyin Halittun Jini; da Shiga Cikin Tsarin Kudi da Bankin Musulunci.

(NAN)

Comments
Loading...