For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

CUTA BA MUTUWA BA (1)

Sodikat Aisha Umar

**************************************

Barci nake muraran, kwatsam sai ji nayi cikina yana kullewa, ji nake duk cikin mafarki da nake ne, amma ga mamaki, ina bude idanuwana na ji tabbas ba mafarki bane gaskiya ne.

Ji nayi cikina ya kara kullewa yayin da kwanciya ta gagare ni, na durkushe a kasa hade da dafe saitin inda yake min ciwo. Kasancewar ni kadai ce acikin dakin yasa babu wanda ya san ina yi bare ya kawo min dauki, na fi minti 10 acikin wannan yanayin sannan cikina dake ciwo ya lafa.

Ganin ya lafa yasa na mike na nufi sib din dakin, inda nake ajiye wayata, na shiga kiran layin mahaifiyata. Bugu biyu ta daga hade da yin sallama, amsa sallamar nayi sannan ta dora da cewa.

“Basma ya kike?”

“Lafiya kalau.” Na fadi tare da ya mutse fuska tamkar ina gaban ta. Jin shuru yasa ta cewa.

“Hello…Hello Basma ba kya jina?”.

Ajiyar zuciya na sauke, sannan na ce da ita; “Ina jinki Umma.”

“Haba Basma, dama kina jina kika yi shuru? shin akwai abin dake damun ki ne?

Sosa kai nayi hade da fadi cikin zuciyata, “ni kam ni nake da damuwa domin mai daki shi yasan inda yake masa yoyo,” amman a fili nayi karfin halin cewa; “a’a babu komai Umma.”

“Uhmn! Basma kenan, ko karatu ne ya sa yanayin muryar ki canjawa?”

“Umma kin dai damu, bana dan jin dadin jikina ne.”

“Ayya sannu, wata kila malaria ce tunda ke bakya kaunar kwana a gidan sauro wanda ba karamin kariya yake bayarwa ba daga cizon sauro da zai iya saki jinya, ko kuma shan maganin sa duk bayan wata uku amman kin ki, rashin tsaftar muhalli ma kan janyo sauro. Wata kila ma makarantar ta ku babu kyakkyawan muhalli ko?”

“Haba Umma ba fa irin makarantun da kika sani bane makarantar tamun.”

Katseni ni tayi da cewa; “Basma kenan”…

A dai-adai nanne kuma katin wayata ya kare.

Komawa kan gado nayi, tare da tunanin wasu iyayen da suke bawa yayansu magani kai tsaye ba tare da shawartar likita ba.

Jin sautin wayata ne yasa ni dawowa daga duniyar da na luluka a yan mintinan da suka shude, hade da kallon gefen da wayata take. “Everlasting Mom” sunan dake yawo a kan fuskar wayar, da sauri na daga ganin Umma ce ta biyo kiran.

Sallama nayi ta amsa, sannan ta shiga bani labarin irin rayuwar da take fuskanta a gidan iyayenta, domin tun bayan rasuwar mahaifina muka koma gidansu da zama, ganin ba mu da karfin da zamu iya cigaba da biyan kudi hayar da muke ciki, rana a tsaka muka tattara kayan mu muka koma.

Da farko mun fara zaman farinciki daga bisani muka dawo sai zaman bawa juna hakuri, barin ma ni da koda takalmin wata na dauka da niyyar shiga bayi domin watsa ruwa sai a goranta min. Haka ce ta sa ni rana a tsaka na hada kayana, na koma gidan kawuna.

Ina tausayin mahaifiyata ina tausayin kai na, domin mun ga rayuwa ko kuma na ce muna kan gani ma, tunda ni farin cikina shine makaranta, bakin cikina kuwa shine gidan kawuna, “Wai an gudu ba a tsira ba”, duk da rayuwar nan sai anayi ana bawa juna hakuri, “tunda harshe da hakori ma akan samun sabani watarana.”

Mahaifina Mallam inuwa mai karamin karfi ne, domin faskare yake na itace, matan mahaifina uku yara kuma goma sha uku, ni ce yarsa ta farko haka ma a gurin mahifiyata kuma ni kadai, kasancewar ta samu matsala a mahaifarta tun sa’adda kari wato fibroid ya futo mata aka yanke, shikenan ya zamana koda yaushe suna futowa ana yankewa, wadda haka yasa likita shawarta mu kan kawai a yanke mahaifar a huta, haka kam akayi aka yanke mata mahaifar, sannan ta samu sallama daga ciwon cikin da ya sako ta a gaba.

Yawancin likitoci na danganta futowar Karin mahaifa da yawan cin jan nama wasu ka ce daji ne, amma bincike ya nuna daji baya kawo Karin mahaifa, sai dai akan iya gadar ta. Shi yasa mafi yawancin lokuta likitoci kan shawarci al’umma da rage cin jan nama domin bashi da kyau sosai a jikin dan Adam, wanda ma ake gani zai iya yiwa dan Adam amfani a jiki shine naman kaza.

Mun a gidanmu jan nama sai Sallah-Sallah idan makota sunyi, sai su kullo mana shi a leda a kawo gidan mu sadaka.

Naman kaza kuwa ni tunda na taso ban taba ganin an ci ba, sai dai idan har daya daga cikin matan mahaifina suka haihu, sai a siyo kai da kafa da hanjin kaza ayi dahuwar kalwa a dan sammana kwaya dai-dai.

Mahaifina Mallam Inuwa ya rasu sakamakon jinyar ciwon sugar wanda ake kira da diabetes, mahaifina ba mai bin ka’idojin likitoci bane, domin akan bawa masu irin wannan jinyar ka’aidoji, kama daga abincin da za su ci, ko kuma lokacin su na ziyarar likita domin duban hawa da saukar suga. Don magance wata matsalar idan har akwai kafin ta zama babba.

Ba irin shawarar da ni kaina ban baiwa mahaifina ba,  amman yaki domin a cewar sa, shi ya fi son yaci ko ma mainene domin a dauki gawarsa da nauyi idan har ya mutu, shiyasa baya bin shawarwarin likitoci sai dai in ganin sa yayi kwance magashiyan akan gado ba lafiya.

Wataranar Alhamis, ina wanke-wanke a bakin famfo dake kusa da kofar fita daga gidamun, sai ga mahaifina ya shugo yana jan kafa jini na zuba a dan karamin yartsan sa, bansan sa’ada na kwala ihu ba, har matan gidan mu da yaransu da mahaifiyata suka futo suka ganewa idanuwansu, gami da rikicewa fiye da yadda nayi.

Baba muje asibiti dan Allah tun kafin taitaunus ta shiga cikin ciwon, domin an sha gayamana a makaranta ko da dan karamin ciwo kaji kaje a maka allurar taitanus, barin ma kai da kake da ciwon suga. Na karashe maganar da kwala.

Ya mutse fuska yayi sannan ya dubeni ya ce.

 “je ki ki daukomin reza da tsumma”.

 Ah! kame baki nayi cikin kuka na ce.

Haba baba mai yasa baza ka yarda muje chemist ba, a maimakon ka cire itacen da ya sarin kafar ka da kanka. Muryar mahaifiyata na ji tana cewa.

 “ basma ki bi umarnin sa.”

Haka yasa ni juyawa na je na dauko wuka da tsuman banda reza domin wata tsohuwa na gani, kuma a sha fadakarwa kan babu kyau amfanin da rezar da wani yayi amfani.

 zuciyata na bugun uku-uku na bashi abin da ya nema, gami da rufe idanuwana, jin sautin  karan da ya saki ne yasa ni bude idona, domin banza iya jurar ganin jinin dake zuba daga dan yatsan kafarsa ba.

Cikin kwalla na karasa gun da yake, yana shirin daura tsumman a kafarsa na rike yayin da yace.

” Wash!”

 Sannu Baba, dan Allah ka bari muje asibiti wannan abin da kake tunani karami ne sai ya zaman bab..babban.

Da in’ina, na karasa magana ta. Kwace tsuman dake hannuna yayi ya kule kafarsa da ke famar zubar jini sannan ya juyo gareni yace.

 “Basma kin damu da muje asibiti, ina da kudi ne? da ina dashi ai da naje kodan saboda radadin da ciwon  yake min, dan haka ki kyaleni. Ni nasan mai nake ji, kuma dan Allah kowa ya koma ya cigaba da uzirin sa.”

 Haka yasa mun tasewa kowa ya koma inda ya futo.

Bayan kwana biyu kafar mahaifina ta kumbura sosai, shi Kansa mahaifina ya kumbura ya zamana sai ni da mahaifiyata ne muke kwantar dashi mu mikar dashi sauran matan suka juya mana baya tare da yayansu.

Rashin fitarsa ya janyo mana rashin dora sanwa a gida, domin shine wani babban bango a gidan mu da muke jingina ko min rashinsa. Kasancewar haka yasa ni sai dai na dauki kwano naje nayi bara kamar yadda almajirai ko yan gudun hijira keyi, wasu lokuta na samo mana abin da zamu ci wani lokacin mu kwana haka. Sanin kowa ne cewa bara ta mamaye yankin Arewancin kasar nan ta Nigeria saboda wasu manyan matsololin da suka mamaye mun kamar, taulauci, karancin karantu, shaye-shaye, rashin tsaro da sauran su.

 Bayan kwana hudu mahaifina yace ga garin ku.

“Basma! Basma!”

A firgice na ce, “na’am Umma.”

Ganin waya a kunnena yasani tunawa da waya nake, na luluka duniyar rayuwata, ta baya, maida hankalina nayi akan wayar, na juyo Umma na cewa.

“Magana fa nake miki tun dazu kinyi banza dani ko har yanzu jikin naki ne?

“A.a” nace mata.

Kara jefa min tambaya tayi ta ce; “Ko lecture zaki shiga?”

Murmushi nayi na ce. “Eeeh Umma”.

Hakane ya sa ta cewa sai ajima tare da min yan nasihohin da akoda yaushe takan min kafin ta kashe waya.

“ki kula da kanki, ki tsare mutuncin ki, sannan abin da ya kai ki makaranta ki tsaya kiyi shi, ki dubi Allah Basma karki bani kunya ki biyewa kawayen banza, kuma ki iya rike talaucin ki, komai mai wucewa ne, *watarana sai labarin, mai labarin ma ba za a samu ba*”

Sannan ta kashe wayarta

Ku buyomun acikin Littafin Cuta Ba Mutuwa Ba domin ji ya rayuwar Basma take a makaranata, shin tana nutsuwa tayi abin da ya kaita? Shin littafin zai amsa sunan shi Cuta Ba Mutuwa Ba? Ku cigaban da kasancewa damu a wannan shafin na mu domin hausawa sun ce *gani ya korin ji*….

Ni ce ta ku har kullum Sodikat Aisha Umar Memalari mu hadu a littafin Burin Kowane dan Adam idan Allah ya kaimu gobe a wannan shafin.

Comments
Loading...