For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

DA ƊUMI-ƊUMI: ECOWAS Ta Baiwa Sojojin Nijar Mako 1 Da Su Dawo Da Bazoum Kan Mulki

Mambobin ƙungiya ECOWAS a yau, sun bayar da wa’adin kwanaki bakwai ga sojojin Nijar da su dawo da bin tsarin mulkin ƙasar da kuma maido da Shugaban Ƙasar Muhammad Bazoum kan karagar mulki.

Wannan umarni na shugabannin ƙasashen Afirka ta Yamma dai na zuwa ne a zaman da suka yi yau Asabar a Abuja domin tattauna abubuwan da suke faruwa a ƙasar Nijar.

Labari Mai Alaƙa: Cikakken Bayani Kan Sabon  Shugaban Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani

Bayan sun jaddada goyon bayansu ga Bazoum a matsayin shugaban ƙasar Nijar da suka yarda da shi, mambobin sun kuma amince da rufe duk iyakokin ƙasashensu da Nijar tare da dakatar da zirga-ziragar jiragen haya zuwa ƙasar.

Da yake sanar da matakin da mambobin suka ɗauka, Shugaban Hukumar ECOWAS, Omar Touray ya ce, dukkan hafsoshin sojojin ƙasashen ECOWAS zasu shiga tattaunawa domin su tattauna kan yanda za a dawo da Bazoum kan karagar mulkin Nijar.

Sai dai kuma tuni sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar suka saki gargaɗi kan shigowar ƴan ƙasashen waje cikin rigimar ƙasar, inda suka ce waɗanda zasu yi hakan kan iya jawo asarar rayukan ƙasar ta Nijar.

Comments
Loading...