For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

DA ƊUMI-ƊUMI: Tinubu Ya Sha Ƙasa A Kotun Amurka, Yayin Da Kotun Ta Umarci Jami’ar Chicago Ta Bayyana Wa Atiku Bayanan Karatunsa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sha ƙasa a ɗaukaka ƙarar da yai a Kotun Yankin Arewacin Illinois ta Jihar Chicago a Amurka yana buƙatar da a dakatar da Jami’ar Chicago sakin bayanan karatunsa ga Atiku Abubakar.

A hukuncinta kan buƙatar Tinubu ta gaggawa a ƙara mai lamba 23 CV 05099, Alƙaliya Nancy L. Maldonado ta yi watsi da ƙalubalantar da Tinubu yai wa hukuncin Alƙalin Kotun Majistare Gilbert kan hukuncin da yai, inda ita ma ta amince da hukuncin na Gilbert gaba ɗayansa.

 A ranar 23 ga watan Satumbar da ya gabata ne, Tinubu ya ɗaukaka ƙara yana ƙalubalantar hukuncin Alƙali Jeffrey T. Gilbert na Kotun Yanki ta Arewacin Illinois ta Amurka wanda ya bayar da umarni ga Jami’ar Chicago, CSU, da ta saki duk bayanan da suka cancanta da suka shafe shi ga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar.

Kafin wannan lokacin dai, kotun tarayyar Amurka da ke Chicago, a lokacin da take hukunci kan ƙarar da Atiku ya shigar yana buƙatar a sahhale masa ganin bayanan karatun Tinubu, kotun ta amince da buƙatar Atikun inda ta ce, Atikun ya iya gamsar da ita game da dalilan da suka sa yake buƙatar bayanan karatun na Tinubu.

Tinubu ya ɗaukaka ƙara yana buƙatar Alƙaliya Nancy Maldonado da hana fitar da dukkan bayanan karatunsa, musamman waɗanda suka shafi batun jinsi da hanyar da ya bi wajen samun shiga jami’ar da sauransu.

A hukuncin da ta yanke a yau Lahadi, Alƙaliya Maldonado ta kotun ta yi watsi da buƙatar Tinubu ta watsi da hukuncin Alƙali Gilbert inda ta tabbatar da hukuncin gabaɗayansa.

Alƙaliyar ta ce, an amince wa buƙatar Atiku Abubakar saboda wa’adin shigar da bayanai kan shari’ar da ke gaban Kotun Ƙolin Najeriya na ranar 5 ga watan Oktoba, 2023.

ƘARIN LABARI: Tinubu Ya Sanar Da Ƙarawa Ƙananan Ma’aikata Naira Dubu 25 A Tsawon Watanni 6

Saboda haka, ta umarci Jami’ar Chicago ta bayar da dukkan bayanan da suka shafi buƙatar Atiku Abubakar zuwa nan da ƙarfe 12 na ranar gobe Litinin, 2 ga watan Oktoba, agogon Chicago.

Alƙaliya Nancy ta jaddada cewar duba da wa’adin 5 ga watan Oktoba na shigar da bayanai a Kotun Ƙolin Najeriya, kotun ba zata ƙara tsayin wa’adin da ta bayar ba.

Atiku Abubakar dai na ƙalubalantar cancantar Bola Ahmed Tinubu ta zama shugaban ƙasa duk da nasarar da ya samu a zaɓen ranar 25 ga watan Fabarairu, inda Atikun ya ce, Tinubu ya gabatar da takardun bogi ga Hukumar Zaɓen Mai Zaman Kanta, INEC, yayin neman takara.

Hukumar zaɓen dai a ranar 1 ga watan Maris ta bayyana Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen, inda Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya zo na biyu, yayinda Peter Obi na jam’iyyar Labour Party ya zo na uku.

Comments
Loading...