An hango wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da PDP na jihar Jigawa da wasu manyan jam’iyyar NNPP, lamarin da ake ganin tamkar zasu sauya sheka ne.
Cikin wadanda aka hango a wasu hoto tare da wasu yan jam’iyyar NNPP hadda Sanatan Jigawa ta Tsakiya Sabo Muhammad Nakudu, da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa a lokacin mulkin PDP, Alhaji Ahmad Mahmud Kulkuli, sai kuma tsohon dan Majalisar Wakilai, Bashir Adamu Jumbo.
Kawo yanzu dai ba a tabbatar da matsayar wadannan yan siyasa ba, amma masu sharhi kan al’amuran siyasa na ganin zasu iya canja jam’iyyunsu ne.

Ana ganin cewa, rasa takara da wadannan manyan ƴan siyasa suka yi ne yasa suke kokarin ballewa daga jam’iyyun nasu na asali.
Idan dai ba a mantaba, Sanatan Jigawa ta Tsakiya, Sabo Muhammad Nakudu, ya nemi tsayawa takarar gwamnan Jihar Jigawa a APC, inda ya zo na biyu, kazalika shima Bashir Adamu Jumbo ya nemi tsayawa takarar a PDP amma kuma ya janye takararsa kafin zaben fidda gwani, sannan Alhaji Ahmad Mahmud Kulkuli ya nuna sha’awar fitowa takarar gwamnan Jihar Jigawan shima a APC amma bai kai ga samun nasara ba.
Bayan ganawar da aka rawaito sun jera kwanaki biyu sunayi, har kawo hada wannan labari, babu wata sanarwa daga manyan ƴan siyasar ko mukarrabin daya daga cikinsu dangane da matsayarsu a jam’iyyar da ake hasashen zasu iya yin kaura zuwa ita wato NNPP.