Tsohon Gwamnan Jihar Plateau, Sanata Joshua Dariye, da tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Jolly Nyame da wadansu mutane biyu sun shaki iskar ‘yanci a yau bayan an sakesu daga gidan yari.
A ranar 14 ga watan Afrilu na wannan shekarar ne, Majalissar Kasa, karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta amince da yin afuwa ga wasu masu laifi tare da shirin fitar da su daga gidajen yari, abun da ya jawo cecekuce.
Lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Yari a Abuja, Chukwuedo Humphrey, ya tabbatar da sakin ga wakilin jaridar PUNCH a tattaunawa ta kan waya.