For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

DA DUMI-DUMI: Firaministar Birtaniya Ta Sauka Daga Muƙaminta

Firaministar Birtaniya Liz Truss ta sauka daga muƙaminta bayan kwana 45 da hawa kan mulki.

Ƴan majalissa na jam’iyyar Conservatives sun buƙace ta da ta ajiye mulki bayan da gwamnatinta ta ci karo da matsaloli.

Ajiye muƙamin nata ya zo ne bayan da wata minista mai matuƙar muhimmanci ta ajiye aiki, yayin da ƴan majalisa na jam’iyyar Conservatives suka yi mata bore.

Liz Truss a jawabinta a gaban fadarta ta ce “Mun tsara manufa ta rage yawan haraji da habbaka tattalin arziki domin cin gajiyar yancin Brexit. Na fahimci cewa a yanayin da muke ciki, ba zan iya sauke nauyin da aka dora min ba a matsayin zababbiyar shugabar jam’iyyar Conservative”.

 “A don haka na gana da Mai alfarma Sarkin Birtaniya domin sanar da shi cewa zan yi murabus a matsayin shugabar jam’iyyar Conservative”, in ji Truss.

A watan Satumba ne aka zaɓi Truss a matsayin firaminista, sai dai kwarjininta ya yi ƙasa bayan soke wasu daga cikin tsare-tsaren da ta ɓullo da su.

Yanzu Liz Truss ta zamo firaminista mafi ƙarancin wa’adi a tarihin Birtaniya – wanda yake biye mata shi ne George Canning, wanda ya yi kwanaki 119 kafin rasuwar sa a shekarar 1827.

Gwamnatin Truss ta fara tangal-tangal ne bayan da ministan kuɗi na ƙasar, Kwasi Kwarteng ya ajiye muƙami, lokacin da ƙaramin kasafin kuɗin da ya gabatar ya rikirkita ɓangaren kuɗi na Birtaniyar.

BBC Hausa

Comments
Loading...