For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

DA DUMI-DUMI: INEC Ta Ce A Binciki Tare Da Gurfanar Da Kwamishinan Zabe Na Adamawa

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta bukaci Sufetan ‘Yansanda, Alkali Baba da ya binciki dakataccen Kwamishinan INEC na Jihar Adamawa, Barr Hudu Yunusa Ari, bisa rashin bin ka’ida wajen sanar da Aishatu Dahiru Ahmed wadda aka fi sani da Binani a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan jihar.

Hukumar ta yanke wannan hukunci ne a zaman da tai yau Talata domin tattaunawa kan turka-turkar da ta taso bayan kammala zaben gwamna a Adamawa.

Hukumar ta INEC ta rubuta a shafinta na Twitter cewa, “A zamanta na yau, 18 ga Afrilu, 2023, Hukumar ta tattauna kan batutuwan da suka taso a game da zaben gwamna a Adamawa, sannan ta yanke hukunci kamar haka:

“1. Rubutawa Sufeton ‘Yansanda domin bukatar gaggawa ta bincika da gurfanar da Kwamishinan INEC na Jihar Adamawa, Barr. Hudu Yunusa Ari.

“2. Bukatar Sakataren Gwamnatin Tarayya da ya jawo hankalin masu alhakin nada kwamishinan INEC kan halin rashin biyayya ga ka’idojin aiki domin daukar mataki na gaba.

“3. Za a ci gaba da tattara sakamakon zaben Adamawa a lokacin da Jami’in Tattara Sakamakon Zaben Gwamna na Jihar ya sanar.”

Comments
Loading...