Sarauniya Ingila Elizabeth ta mutu a yau Alhamis bayan fama da jinya.
Ta rasu ne a Balmoral inda za a mayar da ita London gobe domin yi mata jana’iza.
An haifi Sarauniya Elizabeth ne a ranar 21 ga Afirilu, 1926 a Bruton Street da ke London.
Ta zama Sarauniyar Ingila bayan ta gaji mahaifinta a ranar 6 ga Fabarairu, 1952.
Elizabeth ita ce wadda ta rike sarautar Ingila mafi tsawon lokaci, domin kuwa ta shafe shekara 70 da wata 7 tana kan gadon sarauta.