For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

DA DUMI-DUMI: Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Kasa Ya Ajjiye Mukaminsa

Shugaban Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Farfesa Rufai Alkali ya mika takardar ajjiye aiki a matsayin shugaban jam’iyya na kasa.

Alkali wanda ya bayyana hakan a jikin wasikar da ya turawa Sakataren Jam’iyya na Kasa, ya alakanta hukuncin saukarsa domin bayar da dama ga sabbin jini domin su gina a kan ci gaban da jam’iyyar a dan takaitaccen lokacin da ya debe yana shugabantar jam’iyyar a kasa.

Wasikar ajjiye aikin na da taken, “Wasikar Ajjiye Aiki na Matsayin Shugaban Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party na Kasa”, sannan a cikinta an rubuta, “Ina farincinkin rubutawa tare da turowa gare ka cewa na sauka daga mukamin Shugaban Jam’iyya na Kasa, farawa daga ranar Juma’a 31 ga watan March, 2023.

WANI LABARIN: Kotu Ta Yanke Wa Mutane 3 Hukuncin Rataya A Jigawa

“Duba da abubuwan da suka faru kafin, lokacin da kuma bayan manyan zabubbuka da aka gudanar a ranakun 25 ga February da 18 ga March, 2023, ra’ayina ne cewa NNPP tana da gobe mai kyau da kuma karfin iya zama siyasa ta kan gaba da ke da karfin iya cin zaben shugaban kasa da sauran zabubbuka a 2027.”

“Domin samun nasarar hakan, dole ne mu yi zuzzurfan tunani da kuma tsari. Kuma yanzu ne lokacin yin hakan. Jam’iyyarmu mai girma, New Nigeria Peoples Party zata bukaci gyare-gyare manya-manya kuma masu muhimmanci da kuma sake hadeta a dukkan matakai domin ta kafa turakanta, ta bunkasa aiyukanta, sannan kuma uwa uba ta kara karfin nasararta a kan sauran jam’iyyu 17 da ke jerin jam’iyyun da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta amince da su.

“Tunda, mu a matsayinmu na jam’iyya, duk mun yarda kuma muna da niyyar samar da Najeriya mai inganci karkashin jagorancin kwararren jagoranmu, Sanata Rabiu Kwankwaso, na yarda cewa babu abin da zamu hakura da shi da zai zama mai girma a kan manufarmu.

“Na yarda cewa wannan canji zai fara daga kaina. Wannan a takaice shine dalilin da ya sa na yanke hukuncin komawa gefe daga ofisihin Shugaban Jam’iyya na Kasa domin bayar da dama ga sabbin jini su karbi jagorancin su gina kan gudunmawar da muka bayar. Na yi fatan a ce na yi fiye da haka.

“Da wannan wasika, ina son na sanar da Jagoran Jam’iyya kuma Dan Takarar Shugaban Kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso, mambobin Kwamitin Shugabancin Jam’iyya na Kasa da dukkan mambobin jam’iyyarmu cewa, ina nan kuma zan ci gaba da kasancewa a matsayin mamba na jam’iyyarmu, kuma na yi alkawarin zai yi aiki da kuma bayar da goyon baya ga jam’iyyarmu a dukkan matakai domin tabbatar da ci gaba da bunkasar jam’iyyarmu.”

Comments
Loading...