Dan takarar neman kujerar Shugaban Kasa a jamíyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya baiyana cewa, da yanzu tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi ne ke yi masa takarar Mataimakin Shugaban Kasa.
Kwankwaso, wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano ne, ya yi wannan jawabi ne jiya Litinin a Kano kan rade-radin da ake na cewar, sabon dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar Labour Party zai zama mataimakinsa a takara.
“Mutane da yawa sun kawo shawarar hakan. Na yi imani da hakan ta faru ba don ya shiga wata jam’iyyar ba, yanzu kuma ya riga ya zama dan takarar Shugaban Kasa kamar yanda muka gani a labarai yanzu,” in ji Kwankwaso a lokacin da ake hira da shi a gidan Talabishin na CHANNELS.
“Yanzu dai zamu ga mai zai je ya zo a cikin ‘yan kwanaki ko ‘yan makonni.”
Da yake yi wa Peter Obi fatan alkhairi, Kwankwaso ya ce su biyun suna da damar tattaunawa kan abubuwa da dama da suka shafi kasa.
“Tabbas, mun samu dama ta mu fadawa kan mu abubuwa da dama da suka shafi kasa har zuwa ‘yan kwanakin da ya sanar da shigar Labour Party wadda a yanzu ya zame mata dan takarar Shugaban Kasa,” in ji shi.
Da ake tambayarsa ko jam’iyyarsa zata duba yiwuwar daukar abokin takararsa daga daga yankin Kudu maso Gabas na Inyamurai, Kwankwaso ya ce, har yanzu NNPP ba ta yanke komai a kan hakan ba. A matsayinsa na tsohon jagora a APC, ya ce akwai bukatar NNPP ta samu wani dan takarar Shugaban Kasa wanda zai kasance mai tasiri.
Kwankwaso ya yi karin bayani kan hakan, “Har yanzu ba mu zo nan ba. Bayan taron fidda gwani, jam’iyya zata zauna ta duba ta gani ko zamu samu kyakkyawa kuma ingantacce, mai kwarewa; wani wanda yake da karbuwa; wani wanda zai iya kawo mutane da dama su zabi jam’iyyarmu a matsayin Mataimakin Shugaban Kasa a NNPP daga bangaren Kudancin kasar nan.”