
Ƙungiyar Ci Gaban Tattalin Arziƙin Africa ta Yamma, ECOWAS, ta bayar da umarni ga sojojinta da ke jiran umarni da su farmaki masu juyin mulki a Nijar domin dawo da amfani da kundin tsarin mulkin ƙasar.
Jagoran ECOWAS, Omar Alieu Touray ne ya bayyana hakan a lokacin da yake karanta jawabin bayan taron da suka gudanar kan Juyin Mulkin Nijar, yau Alhamis a Abuja.

Cikin waɗanda suka yi zaman na yau, akwai Shugaban ECOWAS kuma Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Sauran sun haɗa da shugabannin ƙasashen Guinea Bissau, Senegal, Cote ‘d’Ivoire, Ghana, Benin, Sierra Leone, da Togo, yayin da ƙasashen Liberia da Gambia suka turo wakilcin ministocin ƙasashen waje.
A yau ne kuma sojojin da ke mulkin Nijar, suka sanar da kafa sabuwar gwamnati wadda suka naɗa Ali Mahaman Lamine Zeine a matsayin firaminista da kuma wasu ministocin guda 21.