For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

DA ƊUMI-ƊUMI: NLC Za Ta Yi Yajin Aikin Gargaɗi Na Kwana Biyu A Farkon Mako Mai Zuwa

Ƙungiyar Ƙwadago, NLC, za ta fara gudanar da yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyu a ranar Talata, 5 ga Satumba, 2023 saboda nuna rashin jin daɗinta ga gwamnati na gazawa wajen magance raɗaɗin ƙuncin rayuwar da janye tallafin man fetur ya jawo a kan ƴan ƙasa.

Shugaban NLC, Joe Ajaero ne ya bayyana hakan a yau Juma’a, a ganawar da yai da manema labarai a ofishin ƙungiyar da ke Abuja, a matsayin matsayar da ƙungiyar ta ɗauka a zaman da tai a jiya.

A KARANTA WANNAN: Tallafin Naira Biliyan Biyar Ba Zai Magance Talauci Ba, In Ji NLC

A watan Agustan da ya gabata ne, NLC ta gudanar da zanga-zangar nuna ƙin amincewa da tsare-tsaren yanda gwamnati ke tafiyar da yanayin da janye tallafin man fetur ya jawo a kan ƴan Najeriya.

Tun dai ranar farko ta mulkinsa, ranar 29 ga watan Mayu, 2023 ne Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya janye tallafin man fetur abin da ya sanya man yin tashin gwaron zabi daga naira 185 zuwa naira 610 a yanzu.

Duk da cewar, gwamnatin Tinubu ta kafa kwamitin da zai ɓullo da hanyoyin magance raɗaɗi ga ma’aikata, ƙungiyar ƙwadagon ta gano cewar har kawo yanzu kwamitin bai shirya komai game da hakan ba.

Comments
Loading...