Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da ƙirƙirar sabuwar Ma’aikatar Gwamnatin Tarayya kan Harkokin Kiwo.
Shugaban ya bayyana hakan ne yau Talata lokacin da yake ƙaddamar da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Inganta Harkokin Kiwo a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Kwamitin na ƙarƙashin shugabancin Shugaban Ƙasa da kuma tsohon shugaban Hukumar Zaɓe, INEC, Attahiru Jega a matsayin mataimakin shugaba.
Ana sa ran kwamitin ya gabatar da shawarwari waɗanda idan aka yi amfani da su zasu wanzar da zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma tare da tabbatar da tsaro da wadatar tattalin arziƙin ƴan Najeriya.