For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe ‘Yan Ta’addan Da Suka Kai Hari Sansaninta Na Sokoto

Rundunar Sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kashe dimbin ‘yan ta’addar da suka kai hari sansanin soji na Sokoto.

Manjo Janar Benjamin Olufemi Sawyer, Daraktan Yada Labarai na Sojojin, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce sojojin Operation Hadarin Daji, tare da sauran hukumomin tsaro, sun yi nasarar dakile harin da ake zargin kungiyar Islamic State for West Africa (ISWAP), ‘yan ta’adda da’ yan bindiga a Burkusuma a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

A cewarsa, harin da aka kai da misalin karfe 5:30 na safe, 26 ga Satumba, 2021, a kan iyakar Najeiya da Jamhuriyar Nijar, sojoji sun dakile shi cikin hanzari.

“Sojojin Operation Hadarin Daji tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, sun yi nasarar dakile wani hari da wasu‘ yan ta’adda da ake zargin ‘yan ISWAP da ‘yan bindiga da kaiwa a Burkusuma da ke karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. ,” In ji shi.

“Harin da bai yi nasara ba, wanda aka yi da misalin karfe 5:30 na safe, ranar 26 ga Satumba 2021, a kan iyakar Jamhuriyar Nijar sojoji sun dakile shi nan take.

“Hare-haren da sojojin Forward Operation Base (FOB) suka kai, kamar yadda aka gani a watannin baya-bayan nan a shiyyar Arewa maso Yamma, ya kasance takura ga ISWAP da‘ yan fashi. Maharan sun zo da yawa, ta hanyar amfani da hanyar sadarwa daga makwabciyar kasar, inda suka kai harin lokacin da sojojin suka fita gudanar da hare-hare a yankin da aka ba su..

“Duk da haka, gaggawar da sojojin suka yi ya taimaka wajen dakile harin yayin da aka kashe da yawa daga cikin mayakan na ISWAP wasu kuma suka sami raunuka daban-daban, wanda hakan ya sa suka bi ta Bassira a Jamhuriyar Nijar.

“Abin takaici dai shine, an sami wasu adadin wadanda suka rasa rayukansu a bangaren sojojin yayin haduwar.

“A halin yanzu, sojojin Najeriya da na Nijar da ke aikin hadin gwiwa a halin yanzu suna bin sawun sauran mayakan ISWAP. Yanzu haka an samar da zaman lafiyar rundunar FOB.”

Comments
Loading...