Ɗaya daga cikin dalagets da suke wakiltar Jihar Jigawa a wajen babban taron zaɓen fidda gwani na Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC wanda ake gudanarwa a Abuja ya mutu.
Dalaget ɗin mai suna Alhaji Isa Baba Buji, ya mutu ne a jiya Talata.
Kafin rasuwarsa, shine Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Jiha a yankin Kudu maso Yammacin Jigawa.
An rawaito cewa, ya faɗi ne a ranar da safe, lokacin da yana masauƙinsa, yana shirin fita filin babban taron.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa, Bashir Kundu, ya tabbatarwa da jaridar DAILY TRUST lamarin, inda ya ce, marigayin ya rasu ne da safiyar Talata.
Ya ƙara da cewa, ya faɗi ne lokacin da yana masauƙinsa a Abuja, inda aka garzaya da shi asibiti, ana zuwa, likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
DAILY TRUST ta gano cewa, ɗan Majalissar Wakilai mai wakiltar Buji/Birnin Kudu, Engr. Magaji Dau Aliyu ne ya kai shi asibitin.