For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Dalibai Na Son JAMB Ta Fadada Bayar Da Damar Yin Rijista

Shugabancin Kungiyar Dalibai ta Najeriya, NANS, a yau Alhamis ta yi kira ga Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB da ta fadada bayar da damar yin rijistar DE a dukkan fadin kasa.

Kiran na JAMB wanda ya fito daga ofishin Mataimakin Shugaban Kungiyar na Kasa, Kwamared Afeez Babatunde Akinteye ya bayyana cewa, kuntatawar da aka sanyawa masu rijistar DE na cewa dole ne sai sun je ofishin JAMB da ke shalkwatar jihohi ba ta dace ba, musamman duba da wadatar ci gaban sadarwar zamani da ake da ita a Najeriya.

Jawabin da aka yi wa take da, “NANS Tana Kira na a Fadada Damar Yin Rijistar DE, Babu Bukatar Dogayen Layuka Da Bata Lokaci”, ya fara da cewa, “Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan Mahasin Idrees, mai shirin yin JAMB wanda ya rasu a ranar 11 ga watan April, biyo bayan mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a hanyarsa ta dawowa daga Kaduna zuwa Zaria bayan ya je cike DE a Kadunan.

“Duba da yanayin matsalar tsaro da lalatattun tituna a Najeriya, masu son cike DE da ke nesa na shiga hatsarin yin doguwar tafiya domin kawai su yi rijista, abin takaicin ma shine, mutum ba shi da tabbacin kammala yin rijistar a rana daya,” in ji Akinteye.

Mataimakin Shugaban Kungiyar NANS ya kuma roki Shugaban Hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede da ya yi amfani da santocin da ke makarantun gwamnati.

Comments
Loading...