Kungiyar Dalibai ta Kasa (NANS) reshen Kasar Ukraine sun rubutowa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wasika inda suke rokon a gaggauta debe daliban Najeriya da ke kasar ta Ukraine.
Wannan na zuwa a tsakanin yanayin yaki da ake gwabzawa tsakanin kasar Rasha da Ukraine wanda kawo yanzu aka baiyana cewa ya lakume rayuka sama da 50.
A baya dai ofishin jakadancin Najeriya da ke Ukraine ya yi kiran cewa a samu nutsuwa inda a daya bangaren kuma yai kiran ‘yan Najeriya mazauna Ukraine da su kula da tsaronsu.
To amma a wasikar da aka turowa Shugaban Kasa mai taken “Bukatar Gaggawa: Wasika Zuwa ga Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari” ta yau Alhamis, daliban sun ce biranen da ‘yan Najeriya ke zaune a ciki a kasar ta Ukraine ana kai musu hari.
Wasikar da Shugaban Kungiyar NANS a Ukraine, Eunice ya sanyawa hannu ta ce, rikicin Rasha da Ukraine ya yi kamari.
Wasikar ta ce, “Gaisuwa ga Shugaban Kasa. Mune shugabannin Kungiyar Daliban Najeriya a Ukraine (NANS-UKRAINE).
“Mun rubuto maka wannan wasika ne game da halin rikicin Rasha da Ukraine wanda yake ta hauhawa zuwa safiyar yau, 24 ga Fabrairu, 2022 inda harbe-harben bindiga da tashin bama-bamai suka mamaye yankin da ‘yan Najeriya ke zaune.
“Muna rokonka Mai Girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ka aiko domin gaggauta debe daliban Najeriya wadanda yanzu haka suke kasar Ukraine. Mun gaskata kuma muna jiran kasarmu (Mafi Girma a Afirka) a wannan matsanancin yanayi.
“Zai kasance karramawa ta musamman idan aka aiwatar da bukatarmu cikin gaggawa kamar yanda muka bukata. Har abada wannan karramawa zata kasance a zukatanmu. Muna gode maka Mai Girma Shugaban Kasa a yayin da muke jiran hukuncinka”.