For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Dalilan Da Suka Sa CBN Ya Amince Bankin Providus Ya Mallaki Bankin Unity

Wasu dalilai sun ƙara bayyana a jiya da suke nuni da abun da ya sa Babban Bankin Najeriya, CBN ya amince da hukuncin cewar Bankin Providus ya mallaki Bankin Unity.

Jaridar THISDAY ta tattaro muhimman abubuwan da babban bankin yai la’akari da su waɗanda suka haɗa da cewar Bankin Unity muhimmin banki ne da bai kamata a bari ya karye ba, saboda ɗinbin masu ajjiya da yake da su a faɗin yankin Arewa.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewar, yawan masu ajjiya a bankin ba shi ne babban abun la’akari ba, sai dai kasancewar Bankin Unity ne kaɗai bankin da yake aiki wa jihohi da ƙananan hukumomin Arewa da dama.

Wannan ne dalilin da ya sa, CBN ya yarda cewar, idan aka bar Bankin Unity ya durƙushe, mutane da dama a yankin Arewa zasu rasa damar amfani da banki.

Ƙari a kan haka kuma, an gano cewar, mafi yawan waɗanda suka karɓi bashi daga Bankin Unity manoma ne, saboda haka karyewar bankin zai matuƙar yin tasiri kan tsarin samar da abinci a yankin da ma ƙasa baki ɗaya.

A makon jiya ne, tsarin hada-hadar bankuna ta girgiza a ƙasar nan, biyo bayan amincewa da haɗewar Bankin Unity da na Providus.

Shi dai Bankin Providus na ƙarƙashin kamfanin Providus Bank Limited wanda Walter Akpani ke jagoranta, wanda kuma ya samu rijista daga CBN a shekarar 2016.

Comments
Loading...