Tsohon Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya kare takarar neman Shugaban Ƙasa da Atiku Abubakar ke yi, inda ya ce, Atikun zai lashe zaɓe a shekarar 2023 da gagarumin rinjaye.
Melaye, a lokacin da ake tattaunawa da shi gidan telebijin na TVC, ya nuna gamsuwarsa ga yanayin yanda aka gudanar da kuma sakamakon zaɓen fidda gwani na takarar Shugaban Ƙasa da jama’iyyar PDP ta gudanar.
Tsohon ɗan Majalissar Dattawan, ya kuma nuna ƙarfin guiwarsa kan ƙarfin da jam’iyyar PDP ke da shi na ƙwatar mulki daga hannun APC a shekarar 2023.
A ganinsa, taron zaɓen fidda gwanin ya samar da ɗan takara mafi can-canta a ingantaccen zaɓe na gaskiya wanda duk ɗan jam’iyyar PDP ke alfahari da shi.
Da yake amsa tambayoyin da akai masa kan canja goyon bayansa daga tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Bukulo Saraki zuwa Atiku Abubakar, tsohon ɗan Majalissar Wakilan ya ce shi bai canza goyon bayansa ba.
Ya baiyana cewa ya goyi bayan Bukulo ɗari bisa ɗari lokacin da suna tare.
“Ban canza goyon bayana ba daga Saraki zuwa Atiku. Ɗari bisa ɗari ina tare da Saraki lokacin da muke tare. Ba ni da wata matsala da Saraki, yau da safen nan ma na ganshi kuma duk mu yiwa juna raha.
“Na zabi Atiku ne a wannan karon saboda ya kamata na tsaya da wanda aka sani. A wannan lokaci, muna buƙatar mai haɗa kai ne, wanda zai iya haɗa kan Najeriya. Wanda ba za a na masa kallon Musulmi ko Kirista ba. Atiku sanannen mutum ne wanda duk ɗan Najeriya ya san shi. Saboda haka na bar wanda ba a sani ba ne na koma wanda aka sani. Saboda haka ban canza goyon bayana ba sai dai kawai na goyi bayan wanda zai bunƙasa Najeriya,” inji Dino Melaye.
Da yake magana kan kayen da ya sha a zaɓen fidda gwanin sake neman komawa Majalisar Dattawa, Melaye ya ce, duk abun da ya faru a wajen zaɓen fidda gwani ya zama tarihi kuma ba ya son tattauna shi a nan gaba.
Ya ce, “Na ɗora gaba kawai. Duk abun da ya faru a neman tsayawa takarar ɗan Majalissar Dattawa ya riga ya zama tarihi. Ba na son abin da ya wuce ya riƙe ni. Wannan zaɓen fidda gwanin ya wuce, ni ma kuma na ɗora a rayuwata.
“A matsayin Sanata, a ɓangaren wakilci, na yi iya bakin ƙoƙarina saboda na aiwatar da aiyuka da dama. A tarihin Majalissar Tarayya, nine wanda ya gabatar da ƙudire-ƙudire mafiya yawa. Bayanan suna nan, kuma ba za a iya canza su ba.”
Ya kuma ƙaryata jita-jitar cewa, Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya yaudari abokinsa kuma abokin takararsa, Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, lokacin da Tambuwal ɗin ya sanar da janyewarsa daga takara tare da buƙatar magoya bayansa da su zaɓi Atiku Abubakar.
Melaye ya ce, Tambuwal bai bijerewa Wike ba saboda babu wata rubutacciyar yarjejeniya da akai tsakanin su biyun.
“Gwamna Tambuwal ya gano buƙatar zaɓar ɗan takarar da zai haɗa kan Najeriya ne, saboda ƙasarmu tana buƙatar wani uba da zai haɗa kan kowa. Wani wanda zai iya haɗa kan Najeriya kuma wannan mutumin shine Atiku Abubakar.
“Alhaji Atiku Abubakar yana kai fin basira da kuma lafiya, ya ƙware a siyasa kuma yana da ilimi mai yawa. Atiku ba zai faɗi ba, zai ci zaɓe da gagarumin rinjaye. Duk abun da APC zata yi da ya shafi maguɗi, Atiku ne Shugaban Ƙasa na gaba a Najeriya. Taronmu ya nuna cewa kan mu a haɗe yake sama da kowanne lokaci. Mun zama babban gida,” inji shi.